'Yan majalisar dattawa da na wakilan Najeriya sun hada guiwa in da suka gudanar da zaman majalisar ranar laraba 22.03.2022 a zaure guda, domin kalubalantar wani hukucin da ke barazana ga dokar da suka kaddamar.
Mahukuntan sun yi watsi da hukuncin babbar kotun tarayya reshen jahar Abiya, da ta umurci ministan shari'a Abubakar Malami ya goge sashe na 84 (12) na kundin tsarin mulkin 1999, wanda ya haramta ma masu rike da mukamin siyasa tsayawa takara ko jefa kuri'a, kuma ya wajabta ma duk wanda ke neman a zabe shi a 2023 da ya sauka wata shida kafin zabe.
Wannan ya jawo cece-ku-ce har ta kai shugaban kasa neman su yi ma dokar kwaskwarima, abinda kuma su ka ki amincewa da shi.
A makon jiya dai babban mai sa kara na kasa, Abubakar Malami ya fito ya nuna amincewa da hukuncin babbar kotun, in da ya dauki alkawarin goge dokar. To amma kuma masana harkar shari'a sun yi ca kan wannan hukuncin tare da cewa ya sabawa doka. Fitaccen babban lauyan Najeriya Femi Falana, ya bayyana cewa, babban kiskure ne alkaliyar ta tafka.
Ya kara da cewa, "Idan a ka yi duba da waɗannan sassan na kundin tsarin mulkin Najeriya, lallai mai shari'a tayi babban kuskure wajen yanke hukuncin sassa na 66 (1) (f), 107(1) (f),137 (1) (f) da182 (1) (f) domin waɗannan sassan da mai shari'a ta yi amfani da su su na magana ne a kan ma'aikatan gwamnati ba masu riƙe da muƙamin siyasa ba".
Yanzu dai gamayyar 'yan majalisar dattawan da wakilai duk bakinsu ya zo daya in da suka kalubalanci hukuncin tare da shirin gatzayawa kotu.
Comments