Skip to main content

Mai Tsaron Lafiyar Kakakin Majalisar Wakilai Ta kasa Ya Harbe Mai Sayar Da Jarida

 A jiya da yammaci ne dai lamarin ya faru in da daya daga jami'an da ke kare lafiyar kakakin majalisar wakilai na kasa, Femi Gbajabiamila ya yayi harbin da yayi sanadiyyar mutuwar wani mai tallar jarida.

Gbajabiamila ya wallafa a shafinsa na tweeter cewa, yana kan hanyar dawowa ya tsaya wajen don gaisawa da mutane, to sai wasu gungun mutane suka taso masa abinda ya sa masu tsaron lafiyarsa suka yi harbi, wanda ta kai ga samun daya daga cikin masu sayar da jaridun da ke wurin.

Bayanan da TANTABARA ta samu na cewa an dakatar da jami'n da ake zargi da yin harbin, har sai an kammala bincike.

Galibin lokuta ana zargin jami'an tsaron Najeriya da yin harbin da kan jawo hallakar mutane, wanda ko kwanan baya irin haka ta faru a Kano in da ake zargin jami'an tsaron 'yan sanda da hallaka wasu mutane uku bisa harbin da ake zargin na kuskure ne.

Comments