Skip to main content

El-Rufai Ya Mika Kokon Bara Ga JAMB Kan Kada Ta Sassautawa Dalibai

Daga Zubairu Ahmad Bashir
Gwamnan Jahar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i ya mika kokon baransa ga Hukuma Shirya Jarrabawar Share Fagen Shiga Jami'a (JAMB) da ta duna rokonsa kada ta ragewa daliban da ke son shiga jami'a makin da ake bukata kafin samun gurbi.

Gwamnan ya shaidawa gidan talabijin na Channels haka ne a wata hira da aka yi da shi. Ya ce ko kusa ba taimakawa daliban hakan zai yi ba face mayar da su cima-kwance. El-Rufa'i ya kara da cewa yankin arewacin Najeriya na cikin halin koma baya a bangaren ilmi kuma tuni aka yi masa zarra a wannan fanni.

A cikin hirar ya roki hukumar ta JAMB Allah-Ma'aiki da kada ta sassautawa kowane dalibi. Abu mafi kyau in ji shi shine su ci jarrabawar da za ta ba su makin da za su iya samun gurbin karatu a jami'o'i da manyan kwalejojin Najeriya.
Idan ana iya tunawa dai an samu mummunar faduwar jarrabawar share fagen shiga jami'a ta bana, in da galibin wadanda suka zana ta suka kasa samun adadin makin da zai ba iya ba su gurbi. 
Wanda wannan ya sa hukumar ta JAMB ta ba jami'o'i damar kayyade makin da za su ba dalibai gurabun karo karatu  da kan su ba  tare da ita hukumar ta kayyade munsu ba.

Comments

Wadanda aka fi karantawa

Gwamnatin Najeriya Ta Shirya Da ASUU

 An kai matsaya tsakanin Kungiyar Malaman Jami'o'i ASUU in da gwamnatin tarayya ta amince da bukatunsu. A jiya jumu'a dai ne suka yi wani zama don ganin malaman sun janye yajin aikin da ya dauki watanni bakwai ana yi. A yanzu dai gwamntin Najeriya ta amince da cire malaman daga tsarin albashi na IPPIS wanda suka jima suna turjiya akai, kuma za ta biya malaman albashin duk watannin da su ke bi. Haka ma ministan kwadagon Najeriya Cris Ngige ya tabbatarwa manema labarai cewa, za a karawa malaman jami'ar alwus da zai kai naira biliyan 35 sabanin yadda yake a da na biliyan 30. Ngige ya kuma ce za a ci gaba da tattaunawa kan sabon tsarin albashi na UTAS muddin an kammala tsara shi. A nasu bangare kungiyar malaman jami'o'in sun yi maraba da wannan yunkuri, in da ake ganin matakin ga alama zai iya kawo karshen dogon yajin aikin da aka dade ana yi.