Tsohon shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya bayyana a cikin wata sanarwa
da ya fitar cewa tawagar jami’an hukumar sun mamaye gidansa na alfarma da aka
fi sani da suna Ma-a-Lago da ke a gaɓar tekun jahar Fulorida.
Rahotanni sun nunar da cewa samamen na da nasaba da wani bincike da ake kan
gudanarwa da ke zargin Mista Trump da riƙe wasu muhimman takardun gwamanati tun
bayan saukar sa daga mulki.
Sai dai Mista Trump ya bayyana wannan mataki da kutsen da ya saɓawa doka, “Babu
wani abu makamancin wannan da ya taɓa faruwa da Shugaban Amurka a tarihance”.
Sashen adana bayanan gwamnatin Amurka ya sanar tun a farko cewa, Mista
Trump bai miƙa wasu muhimman takardu ba da suka haɗa da wasiƙu da ya zama
wajibi duk shugaban ƙasa mai barin gado ya hannunta bayan barin sa mulki.
Jami’an ofishin sun ce sun gano manyan akwatuna 15 a gidan waɗanda ke ɗauke
da muhimman takardun. Daga baya sashen adana bayanan ya shaidawa majalisar
dokokin Amurka cewa kowace akwati da aka gano an yi mata alama da rubutu da aka
bayyana “Bayanan Asirin Ƙasa”; in da aka yi nasarar ƙwace su a lokacin samamen.
Wannan matakin dai ya jawo cece-ku-ce a faɗin ƙasar in da ɗaruruwan magoya
bayansa suka taru a gaban gidansa na alfarma na Mar-a-Lago suna ɗaga totoci
tare da nuna adawa da abinda suka kira bita-da-ƙulli.
Ɗan majalisar wakilan jami’iyyar Republican maidawa, Kevin MacCarthy, ya
nunar da matakin a matsayin wanda ya saɓawa dokokin ƙasara, “Mun gaji da haka. Sashen
Dokokin ƙasa ya wuce gona da iri, in da ba za a iya ci gaba da jure amfani da
ƙarfin mulki ba wajen bibiyar ‘yanadawa”.
A cewar tshon shugana ƙasar wannan ba kome ba ne face yunƙurin hana shi
tsayawa takarar shugaban ƙasa nan gaba, abinda kuma ya ce ba za ta saɓu ba.
Comments