Skip to main content

ASALIN TALAUCI DA MATSALAR TSARO A NIJERIYA.

(Gaskiya É—aci gareta)
DALILAN DAKE SANYA TALAKA CI GABA DA ZAMA CIKIN TALAUCI,  ATTAJIRI YA CI GABA DA ZAMA CIKIN ARZIKI
A shekarar 2007, wani hasashe da ofishin mai kula da hada-hadar  kudi na al'ummar Æ™asar Amurka (Congressional Budget Office) yayi cewar, duk wasu tsare-tsare da gwamnatoci ke aiwatar wa 'yan Æ™asa, attajirai kurum yafi amfana, domin kuwa talakawa na Æ™ara ci gaba da zamowar su cikin talauci ne kawai.
Ga kaÉ—an daga abinda binciken su ya nuna;
TALAKAWA: A tsawon shekaru talatin, samun kuɗinsu ya haɓaka ne da kaso goma sha takwas kacal. (Ma'ana talakan da yake samun dalar Amurka ɗaya a tsawon wancan lokaci, har yanzu baya samun dala biyu)
MATSAKAITA: A tsawon shekaru talatin, samun kuɗin matsakaitan mutane ya ƙaru ne da kashi 40 kacal.
ATTAJIRAI: A tsawon shekaru talatin, samun kuɗin attajirai ya haɓaka ninkin-ba-ninkin da kashi 275. (wannan labari na da matuƙar kyau idan aka haɗa shi da yanayin da talakawan Najeriya suke ciki daga shekaru talatin zuwa yau)
Haka kuma a shekarar 2010-zuwa-2011, lokacin da tattalin arzikin Amurka ya faÉ—i warwas, hasashe ya nuna cewa rashin aikin yi da talauci sun Æ™aru sosai, har ma aka ce Amurkawa miliyan arba'in da shida, waÉ—anda a baya suke da rufin asiri (matsakaitan mutane) sai ga shi su ma suka faÉ—a sahun talakawa. 
Hakan ne ya nuna cewa, a duk Amurkawa shida, biyar talakawa ne, É—aya ne attajiri. 
Mutanen da a baya suke ɗaukar ɗawainiyar wasu, ya zama sun koma ta kansu suke yi. Wannan kuma sai ya haifar da ƙaruwar munanan laifuka gami da rashin kwanciyar hankali a ƙasar.
Har ila yau, a wani bincike da masana siyasar duniya suka gudanar, sun lura da manyan shugabannin duniya masu farin jini wurin mabiyansu, da har ma suka hau karagar mulki cikin soyayyar al'umma maÉ—aukakiya, farin jininsu kan dusashe nan da nan.
Misali, Amurkawa sun zaÉ“i Franklin Roosevelt ne lokacin da suke cikin mawuyacin talauci, tsammanin su da ya hau mulki zai yi Æ™oÆ™arin magance wannan matsala, amma sai a kayi rashin sa'a, ya tunkari yaÆ™i tare da Æ™ara tsunduma Amurka cikin Æ™angin karyewar tattalin arziki. 

Haka ma Adolf Hitler, Jamusawa sun lamunce masa ya hau kan mulki saboda suna tsammanin shi kaÉ—ai zai iya warkar da annobar talauci da ta biyo bayan yaÆ™in duniya na É—aya, amma da hawansa sai ya Æ™ara cusa Æ™asar acikin yaÆ™in da yafi na baya tsamari. 

To fa fiye da haka zamu fuskanta muddin matsalar Najeriya ta dore.
Shakka babu, Najeriya kasa ce bahaguwa, mai jama'a da tarin bambancin fahimta, kabilanci da son iya yi, wanda a galibin lokuta kan kai mu ga koma bayan da kan zama babbar nadama.
Misali, almubazzaranci irin na 'yan siyasa da kan kwashi kudin talaka su je Turai da Amurka su sayi gidaje da kadarorin da ba zasu amfane su ba.
Alhali talakawa na zaune cikin wahala da talauci da wurin kwanciya mai munin gaske. Ga su da yara kanana da ba su yi laifin kome ba face dai an haife su a kasa da masu jagorancinta ke shan jininsu. Abinda zai iya saka ka hawaye idan ka gan su
Shuwagabannin farko, irin su Firimiyan  lardin arewa na lokacin, Sardaunan Sakkwato Ahmadu Bello da Abubakar Tafawa Balewa da Nmandi Azikiwe, da 'yan siyasar arewa na farko tamkar su Malam Aminu Kano da Sa'adu Zungur da Malam Mudi Sipikin da dai sauran su, sun gwada misali mai kyau na kishin jama'arsu da kokarin dunke barakar kasa ta hanyar samar da zaman lafiya da salama a siyarsu mai tsafta.
Dubi wannan misali a kasashe irin su Gana da Misira da Afirka ta kudu da ma Kenya, jagororin gwagwarmayar neman 'yanci kamar Nkuruma da Gamal Abdulnasir da Nyerere sun bar misali na gari da 'ya'yan Afirla suka kasa kwaikwaya.
Wannan salon watsi da kishin kasa a bakaken fata kadai ake samun sa, na wariya da kabilanci da son taushe na kasa kazalika da kara ma talauci mizani saman mizani da babu lallai ya fice shi.

Galibin shuwagabanni a Najeriya yanzu haka, kuraye ne: ga tsoro ga sata, ga kuma son zaluntar karami.Misalin haka ana iya ganinsa a siyasar yau, da mafi yawansu suka zama hawainiya ta hanyar yawaita canja riguna ba bisa tartibin dalili ba.
Kaurar da 'yan siyasa da shuwagabannin Najeriya ke yi a yau, ba domin kishin talakawa ne ba, sai domin kishin aljihunsu. A yanayi irin wannan, ya dace talakawa da ke zabar shugabannin, su kauracewa duk wanda ya bar jam'iyarsa da sunan neman mukami.

Ya zama waji a yi watsi da kalamansu masu cike da makida, yaudara da sukarin harshe domin jawo hankalin mabiya da alkawurran da suke yi masu kama da rantsuwar barawo da tasirinsu bai kai ya alewar Makka a bakin yaro ba!
Talauci da matsalar tsaron Najeriya na magantuwa ta hanya daya ne kawai: SANIN DARAJAR KAI!
Ta ya talakan Najeriya zai san darajar kansa?
Wannan tambaya ce da aka dade ana amsawa amma har yanzu mutuwar zuciya ta hana 'yan Najeriya gane wannan. 

Tun farko dai shugabannin yau suka dora mu akan turbar kwadayi da yaudarar kanmu. Sun nuna mana yadda zamu kyamaci juna ta hanyar siyasa. Sun farraka tunaninmu daga baya kuma su bar mu a jam'iyar da suka saka mu, su koma ta wadanda suka nuna muna makiyanmu ne!
To, idan kuwa haka ne me zai sa ba za mu hinjire (ki bin) ga umurninsu ba?
Babban abin kwatanci shi ne yadda kasa irin Sin, wadda ke sahun gaba a yawan jama'a a duniya ta ci gaba, ta kafa gwamnati irin ta tsarin gurguzu mai karfin gaske; tare da shimfida adalci ga miliyoyin 'yan kasa ta hanyar bunkasa noma da kiyo da kimiyya da sauran dangogin tubalan ginin tattalin arziki.
Chana kasa ce mai tsananin hukunci ga barayin dukiyar kasa, da mayaudara, wanda mafi yawan hukuncinta shi ne kisa, domin duk wutar da ba ka kashe ba shakka babu za ta kashe ka!

A Najeriya babu mutum daya daga masu kisan jama'a da aka rataye, haka ma babu hukuncin zahiri da aka zartas ga azzalumai don zama izna, face dai dodorido ko dakan daka shikar daka. 
Kisan jama'a da yawaitar makamai da garkuwa da mutane mata da yara kanana, su ne abubuwan da suka yanke cibi a Najeriya.
A kullum rana za ka ji an kashe mutane tare da kwashe mu su dukiya, amma babu wani gwaggwaban hukunci da aka taba yi wa masu kisan, sai dai ma daure mu su gindi, ta hanyar nan sulhu da ba su shawara da ba su haraji ko wani abu wai wanke mu su kwakwalwa da ba kome ba ne sai makirci da tsoro.

Amurka kan durfafi abokin adawarta don ganin bayansa; wanda a wurinta ta dauke shi barazana ga zaman lafiyarta ko abokan huldarta.
Dauki misalin Saddam Hussaini na Iraki da Osama Bin Ladan Da Kasim Sulaiman na Iran da Mulla Omar da sauran su. Amurka ta murkushe su ba domin addini da akidarsu ba kawai har ma don taskace su da dakatar da su daga cutar da 'yan kasarta.

Koriya ta Arewa da kasashen turai ke harara tare da shata layi tsakaninsu, hadi da musayar kalamai ta hanyar aiwatar da yakin cacar baka a kaikaice, na da hujja da manufa mai kyau, idan ta busa ne don ba makiyanta tsoro ko ankarar da su cewa kankantar damisa raina kama ne ka ga gayya!

Duk wadannan na da alaka da neman kare kai da barazana ga abokan gaba.
Irin wadannan kurari da hankoro ne babu a Najeriya. Mafi yawa jagorori sun fada rami ne mai wuyar fita. 

Kawancensu da galibin kasashen yamma an gina shi ne bisa kadarkon bashi da lamunin da ke da sarka ta hanyar gindaya sharudda ma su alaka da siyasa ko akida da ba kowa zasu amfana ba sai kasashen yammacin turan.

An taba hira da marigayi Sardaunan Sokoto Ahmadu Bello a kafar rediyon BBC  a wajajen 1964, akan manufar wata tafiya da yayi zuwa Burtaniya cewa shin ta shan iska ce ko ta ganin gari?
Sardauna ya kada baki ya ce, "Ai ba a yin tafiyar shan iska da kudin mutane!"
Aka tambaye shi cewa, " galibin kasashen turai na bayar da bashi tare da sarka ko wane irin bashi Najeriya zata ciyo?"
Sai ya ce, "Ba sarka ba ko da labbe (zare) ba za su ciyo bashi ba, diya ne ba bayi ba kuma kan haka zasu mutu. Shi tafiyarsa ta cude ni in cude ka ne, suna da albarkatun kasa kamar gyada da auduga da kuma fatar dabbobi don haka musaya zasu yi da turawa."
Irin wannan ne babu a Najeriya da saurarn kasashen Afirka a wannan latto.

Idan an lura da kyau, zamu iya samun nasara kan matsalar tsaro kadai idan mu talakawa mun daina kashe juna. Mu yi watsi da kwabban da za a ba mu da makamai don kashe 'yan'uwanmu, damar da za ta haifar da rikicin da azzaluman shugabanni zasu yi amfani da ita su farraka mu, su sarrafa mu; su yi muna dodorido da alkawurran baki, da zimmar mu sahalewa burikansu, da zasu yi amfani da su matsayin tsanin ruguza mu duk kuwa da gina su da muka yi da zufarmu da dukiyarmu, kazalika da kalaman bakinmu wajen share mu su hanyar da suka bi suka taka tsanin har suka samu kan su a kololuwa.
Wani marubuci farar fata na cewa, "jefa talakawa a yunwa don ka ji saukin mulkinsu!"
A nasa hasashe, Robert Greene ya wallafa a littafinsa mai suna "48 Laws of Power", wato (Hanyoyin Dubarun Mulki 48).

Wanda shi wannan littafi, an farga cewa da dama daga 'yan siyasar Najeriya a yau na amfani da shi. Su talauta mu, su ki yi mana aiki tare da kwashe kudadenmu, ta haka yunwa da talauci da tsumma zasu tilasta mu bin su tamkar rakumma, domin kawai mu samu abinci da kuncen rigar sakawa.
Kuma wani abin mamaki da takaici shi ne dukiyar mu da berayen suka wawushe suna kaiwa ne a kasashen wancan baturen, wato baya babu zane kenan!

Marubuta da masana adabi sun yi muwafakar cewa, gafalalle shi ne wanda yayi kwance tare da sallamawa cewa tasa ta kare, daidai da hikayar wasu kwadi su biyu abokan juna; da suka fada curin mai. Dayan ya yi kwance ya nutse yana kuka tasa ta kare; dayan ya ci gaba da tsalle cike da fatan samun kubuta wanda watsalniyar ta haddasa daskarewar afararin wuri daya da ya taka tsalle daya sai ga shi waje!
A kome na duniya kada ka sadakas, kai dai ka zama mai naci don kuwa Hausawa sun ce, "A juri kai ungulu kasuwa, wata rana za a samu mai sayen ta"!

Bakar fata na da rauni a fannin ilmi duk kuwa da cewa shi halitta ne mai kwakwalwa da basira.
Dauki misalin larabawa da turawa da yadda suke da gwagwarmayar neman ilmi da yawo da son ganin kwakwaf da ma bincike.
A kasaahen larabawa na zamanin da, Ibn Sina da Ibn Taimiyya da Ibn Batuta dukan su sanannu ne a duniyar kimiyya da addini da ma fasaha.

Idan kaduba littafin H.A.R.GIBB,  "The Travels of Ibn Batuta" (Tafiye-Tafiyen Ibn Batuta) za ku ga tarin bayanai da labaran ilmi da bincike gami da al'ajubba da ya hadu da su a rayuwarsa.

A turawa ma akwai irin su Vasco Da Gama, Christopher Clumbus, Mungo Park, Captain Clapperton, Marco Polo, Green Kirk, Hans Bitcher, R.C. Abraham da Neil Skinner kadan kenan dukan su sun yi yawo da bincike a galibin kasashen Afirka da arewacin turai da Latin Amurka da Asiya.

Bincikensu ya amfane su fiye da shurin masaki, ta hanyar gano mu da yadda muke tafiyar da rayuwarmu: bukukuwa kamar na aure da haihuwa da na kakar amfanin gona da farauta da abinci da sutura da gidajenmu da ma addinanmu.

Wannan ya ba su damar nazartarmu tare da sanin yadda zasu sarrafa mu. Wasunsu ma kamar Hans Bitcher da Skinner da Kirk da Abraham sun ma yi rubuce-rubuce a kan harshe da al'adunmu.

A 1946 R.C. Abraham ya wallafa kamus na Hausa mai suna "The Dictionary of Hausa Language"
Green Kirk ya wallafa "A Grammar of Hausa Language" wanda ya shafi nahawun harshen Hausa.
Littafin farko na Hans Bitcher shine "Rules for Hausa Spelling" (Ka'idojin Rubutun Hausa) da ya rubuta shi a 1910 a birnin Berlin na Jamus.
Niel Skinner yayi rubutu rututu da lissafa su zai ba da wahala, kamar "An Introduction to Hausa Grammar" da "Ikon Allah" daga na 1 zuwa 5 da ya wallafa tare da marigayi Dakta Abubakar Imam da Kamus na Hausa da sauran su.
Idan ka duba zai yi wahala ka kawo bakar fata daya daga Afirka ba ma Najeriya ba da ya zurfafa bincike da yawo irin nasu don gano wata sila ta ilmi, idan ba marigayi Abubakar Ladan Zariya ba (marubucin "Wakar Hada Kan Al'ummar Afirka" da kuma wakar "Al'ajubban Kasar Masar"). Sai dai galibin su kan yi ta hanyar karantar na wasu da aka fi sani da nazari, sannan su wallafa nasu.
Wannan mutuwar zuci da son a ba mu, shi ya haifar muna da hakan yau.
Hasali ma dai, idan muka tafi a haka, babu shakka yau za ta fi gobe.
Irin yadda masu mulki ke fifita iyalansu akan na wasu shi ne abinda babu a kasashen ketare misali turai da Amurka.
Duk yaro da aka haifa a can na kasa ne ba na iyayensa ba. Wani abin ban sha'awa, ilminsa da tarbiyya da samun aiki hakkin hukuma ne, yadda idan aka haife shi, akwai tanadi a bangaren ilmin yaran maza ko mata da lafiyarsu har da samar mu su da aiki. Wanda ya zama wajibi su yiwa wasu yadda aka yi mu su a lokacin tasowa.
Wannan al'adar mai kyau ce muka rasa a kasashenmu na Afirka, musamman Najeriya.
Abu ne mai sauki ka samu mutum da gidan sumunti amma makwabcinsa da darni koda kuwa mai babban gidan na da tarin dukiyar da har tattaba kune ba za su iya canyewa ba.
A Najeriya zaka ga ana odar abincin karya kummalo a Burtaniya, alhali makwabci na neman gayan tuwo ko garin rogo domin kada yaransa bakwai su kwana da yunwa.

A Najeriya kadai zaka ga ana bukukuwan keci raini tare da zubar da dala a kasa ana takawa amma asibitocinmu cike da kananan yara masu neman kudin da za wanke musu koda ko masu fama da cutar daji (cancer) na neman kudin magani ko allura don rage tsananin zafin ciyo da ke sa su kuka lokacin da almubazzarai ke kwasar rawa suna dariya.
Wannan hali na mummunan shugabanci da babu niyyar gyarawa zai haihuwar da maras ido!
Tauye mudu da tsananin tsada, kirkirar farashin da hukumomi ba su sanya ido, kwace filaye da korar ma'aikata; kin yiwa talakawa aikin raya karkara; satar daloli da daurewa 'yan bindiga gindi ta hanyar neman sulhu da su da neman a raba kasa don son mallake dukiya kai kadai, dukan su sun zama ruwan dare da idan ba a taka ma hakan birki ba zasu kai in da babu magani.
Ta ya mai mulki zai koma tamkar an ajiye jariri kan kujera?
Ta ya mai mulki bai bayar da umurnin kwaf daya, yadda sauran kasashe ke yi a zauna lafiya?
Duk kasar da ta zauna babu hukuntawa, la shakka zata zama madaddalar azzalumai da mahara.
Shawarata a nan: talakawa su dawo daga rakiyar jagoran da a zuciyarsa na da burin kai mu ga rami gaba dubu. Kalli misalin shugabancin jaki, da kowa ya bi shi gaba gadi zai hallaka!
Mu kaucewa gishirin baka, ta hanyar ci gaba da watsa musu kasa a ido da yi musu korar kare ba tare da tsoro ba, idan dai muna son gobenmu ta yi kyau.


Comments