Skip to main content

'Yan Jarida Na Shan Ɗauri A Rasha

Wata ‘yar jaridar wani gidan talabijin na Rasha, Marina Ovsynnikova, ta fuskanci ɗaurin wata biyu saboda ta bayyana rashin goyon baya akan mamayar da ƙasarta ke ci gaba da yi wa Yukren.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, wata kotu ta sanar da kama Ovsynnikova da laifin cin amanar ƙasa, sakamakon ɗaga kwalin da ta yi a kusa da fadar Kremlin mai ɗauke da kalaman da ke cewa, “Putin mai kisan kai ne, yara nawa suka mutu sakamakon aikinka, ka gaggauta dakatar da wannan yaƙi”.
Gwamnatin Rasha ta daɗe tana ɗaure masu adawa da mamayar da ta ke yi ma Yukren, tare da bayyana yaƙin  da sunan “aikin dakarun soji na musamman” kuma shugaba Putin ya sha alwashin tsare duk waɗanda aka samu da laifin watsa labarun ƙarya  tsawon shekara goma a gidan jarum.

Comments