A wani zaman sulhu da ake ci gaba da yi a Abuja, gwamnan jahar Rivers Nyesom Wike da tsohon mataimakain jam’iyar PDP na yankin kudu, Chif Olabode George, na cikin sahun gaba wajen ganin jam’iyar ta cire shugabanta na yanzu, Iyochia Ayu daga muƙaminsa muddin a na neman zaman sulhun ya kai ga haifar da ɗa mai ido.
A cewar su, hakan ne kawai zai iya samar da daidaito ga yankin kudancin Najeriya kasancewar ba adalci ne ba ɗan takarar shugaban ƙasa da shugaban jam’iya su fito a yanki guda ba. To, amma kuma wannan buƙata ta gamu da cikas in da a yayin hirarsa da manema labarai a Abuja, Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa, Debo Ologunagba, ya ce ba za ta saɓu ba, domin cire shi kasada ce, da za ta iya jefa PDP cikin sabon ruɗani.
Ya ƙara da cewa, “ai a fili take ƙarara, kamar yadda kundin tsarin jam’iyyar ya tanadar duk lokacin da aka cire shugaban jam’iyya a bisa kowane dalili ne kuwa, to mataimakinsa kan maye gurbinsa kuma ya zama sun fito daga shiya ɗaya. Kazalika, kundin tsarin mulki na jam’iyyar ya sahale samar da maitaimakan shugaban jam’iyya daga shiyoyin kudu da arewa, kenan idan har aka cire Ayu, shakka babu mataimakinsa Umar Damagun wanda ɗan arewa ne daga jahar Yobe, zai maye gurbinsa”.
Ya ƙara da cewa, dole ne a tafi a haka idan har nasarar jam’iyar ake nema domin kuwa wata shida ne suka rage ga soma manyan zaɓukan ƙasa.
Comments