Skip to main content

Barayi Sun Yiwa Ofishin Jaridar Daily Star Nigeria Kaf

A yau da rana wasu gungun barayi da ba a kai ga ganowa ba sun kai samame ofishin jaridar Daily Star Nigeria da ke jahar Sokoto.

Babban editan jaridar, Dr. Mansur Isah Buhari ya tabbatar da wannan lamari, in da ya ce barayin sun yi awon gaba da wasu muhimman kaya da suka hada da kananan kwamfutoci, da akwatin talabijin da ma wasu kudaden da ba a bayyana adadinsu ba kawo yanzu.
Dr. Mansur ya ce, "kamar yadda al'adar ofishinmu ta ke, wakilanmu na wajen nemo labarai ni kai na ma na dan fita bana wajen, lokacin da barayin suka auni hakan tare da fasa kofar ofishin in da suka wawushe kome".
Jaridar Daily Star Nigeria dai na cikin na gaba gaba daga cikin jerin jaridun yanar gizo da ake da su a Nijeriya yanzu haka.

Comments