Skip to main content

Bambancin Bayar Da Labari A Rediyo Da Kuma Talabijin

Shi mai gabatar da shiri a rediyo kullum ya sani sauraren sa ake yi, ba kamar yadda ake kallo a talabijin ba, kan haka dole ya yi amfani da descriptive words, wato kalmomi masu hoto, domin mai saurare ya ga hoton abin a kwakwalwarsa, har ma ya ji dadi a ransa.

Getty images
Ya Misalin Haka Ya Ke Ga Mai Saurare?
Mai saurare na bukatar ganin zahirin hoton abinda mai bayar da labari ke fada. Kunnuwa ke sauraren labarin amma kwakwalwa za ta ci gaba da sarrafa hoton abinda ake siffatantawa. Misalain haka shi ne a suranta maka gida ta hanyar zayyano dukan abinda ya mallaka, kamar kofofi biyu hannun riga da juna da farin fenti sai tagogin gilashi ma su karau-karau ga kuma furanni da aka kawata harabarsa farare da jajaye da kuma rawaya. Nan ta ke kwakwalwar mai saurare za ta dauki hoton har yadda za ku iya ganin sa.

Ga Misalin Haka:
"Gaba daya kankara ta mamaye tsaunukan sun yi fari fat tamkar auduga. A duk shekara irin wannan lokcin sanyi, ruwan gulabe da rafukka kan daskare, za ka gan su kamar gilashi amma fa kasan duka ruwa ne. 
A in da nake tsaye, na hango mafarauntan dabbar nan da ake kira whale da ake samu a manyan tekun kasashen turai ma su tsananin sanyi.

Ma farautan na tafiya a kan wani keke-keken da aka yi da kashi da karnuka shida ke ja saman kankara da gudu, yayin da mutumin ke zaune saman dan keken hannusa rike da igiya tamkar dai akala, yana yi yana girgiza igiyar domin sarrafa karnukan da ke gaba.

Allah Daya gari bamban! Za ka gan su a jere kamar dai yadda ku ka san rakumma, kowane na bin na gabansa, sai dan bambancin shi ne yada suke jere biyu-biyu hannun riga da juna, biyu gaba biyu na biye mu su sai biyu na baya gaba.

Bayan da suka sauka ne domin fede babbar dabbar da suka kashe, na samu zantawa da daya da ga cikin su, wanda ga alamu shekarunsa sun ja, inda na tambaye shi yadda suke yin irin wannan farauta mai ban mamaki".

Ga alama kun soma ganin hoton yanayin wurin da tsaunukan da kankarar da ta lullube su da karnukan watakila ma da siffar dattijon da na soma tambaya?

Bambancin Talabijin Da Rediyo
Kamar yadda na bayyana a baya hakkin mai bayar da labari ne a rediyo ya takarkare wajen bayyanawa mai saurare kusan kome ke wakana, amma fa cikin jimloli marasa yawa. Kuma ya himmatu wajen zabo kalmomi masu hoto da za su taimaki mai saurare ganin abinda ke wakana a kwakwalwarsa, misalin kwallon kafa.
A talabijin hakan ya sha bamban domin labarin tafiya ya ke tare da hoto. Idan mai bayar da labari ya soma magana game da giwa kuma aka nuna giwar a daji, babu bukatar ya ce ga giwa nan a daji mun nuna muku. Mai kallo ya ga giwar ba sai an ce ma sa wannan ce giwar ba. 
Akwai bukatar duk abinda aka ambata a nuna shi lokaci guda, domin mai kallo ya ga abin. Misalin haka shi ne idan mai bayar da labari ya soma magana a kan saka takin zamani a shuka da sassabe ko noma to dole ne a nuna manomi na saka takin. Idan ya ambaci nome shuka ko sassabe ciyawa, shi ma ya wajaba a ga wani abu mai kama da haka, kada a nuna mafarauta janye da karnuka ko 'yan kwallo na gudu a filin wasa.
Ba daidai  ba gasa tsire tare da takalma ko zuba kindirmo a miya!


Comments