Skip to main content

Illolin Amfani Da Rikitacciyar Jimla A Rubutu Ko Rediyo

Papertrue.blog
*"A kokarin hada su da 'yan'uwansu da sanadiyyar rikice-rikice suka rabu."

A yadda harshe ya ke da wuyar sha'ani wajen aikewa da sako, wajibi ne a kaucewa kowace irin jimla mai harshen damo ko mai iya haddasa rudani a kwalkwalwar mai karatu ko saurare.
A maimakon haka ya fi dacewa a ce, "A kokarin hada su da 'yan'uwansu da tashe-tashen hankula suka raba"

Dalili kuwa kalamar rikici ba ta dace da nan ba saboda ko mutum biyu na iya rikici da juna. 
Rikici na nufin jayayya ko rashin yarda da abu da zai iya haifar da rashin matsaya daya, wanda kuma zai kai ga fada. Mutane na iya yin gaba da juna akan rikici na siyasa ko gado.

Amma ita kalmar tashin hankali a bayyane ta ke ga mai saurare, sakamakon irin yadda kalmar ta zama tamkar ta yi kaka-gida saboda yadda yankunan arewacin Najeriya ke fama da tashe-tashen hankula.

Me Ya Kawo Rudani A Nan?
A jimla ta farko mai saurare zai dauka rikicin tsakanin 'yan'uwan ya ke, amma a jimla ta biyu an lura cewa tashin hankalin da ya faru ne ya raba su.
Wace Illa Hakan Kan Jawo?
Sau tari mai karatu ko saurare na iya kasa fahimtar in da maganar ta dosa, saboda ba a fayyace ma'anarta a fili ba.
Misali idan ka ce, "Bala Ya karya ma ta masara".
Za ka saka mai saurare ko karatu a rudu kasancewar ba ka fayyace wanda ya mallaki masarar ba.
Zai fi dacewa ka ce, "Bala ya karya masarar Kande, Ko Bala ya karya ma Kande masararsa".
Fakat!

Comments