Kungiyar Boko Haram ta saki wani faifan bidiyo da ke nuna yaran nan daliban makarantar kimiyya da ke Kankara a jahar Katsina, kwanaki biyar da sace su.
A cikin bidiyon an ga wani yaro mai kimanin shekaru sha biyar na magana cikin Hausa:
"Don Allah ina rokon gwamnati da kada ta yi amfani da duk wasu 'yan sa kai, a rufe dukan makarantu. Kuma sojojin da ke tafe don taimakonmu don Allah su koma, ba za su iya yi wa (mayakan) kome ba". In ji yaron.
A can bayan yaron an ga wasu yara kanana masu yawan gaske da ake umurta da su zauna, kuma da ba su fi shekara goma goma ba, suna kuka tare da rokon a taimaka a cece su daga hannun mayakan.
Faifan bidiyon mai tsawon minti daya ya nuna yaran cikin kura da alamar gajiya a tattare da su, sakamakon tafiya mai nisa a kasa.
Ana kuma jin muryar daya daga 'yan bindigar na gargadin gwamnati da kada ta dauki kowane matakin amfani da karfi. Yana mai jaddada cewa yaran na cikin koshin lafiya.
A ranar jumu'ar da ta gabata ne maharan suka yi awon gaba da daliban, kwana biyu da yin haka mai magana da yawun shugaban kasa akan kafafen watsa labarai Malam Garba Shehu ya fito ya bayyana cewa an soma kokarin ceto yaran, kazalika ba su fi yara 10 ba a hannun 'yan bindigar.
To, amma kuma, wannan faifan bidiyo na cin karo da kalaman na Garba Shehu.
Ranar talatar da ta gabata shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar da wani bidiyo in da ya ke cewa yaran na hannunsu.
Yanzu haka shugaban kasa Muhammadu Buhari na ci gaba da hutunsa
a jahar Katsina wacce ita ce mahaifarsa, kuma har yanzu bai fito yayi jawabi wa 'yan kasa a kan wannan batu ba.
Comments