Yanzu yanzun nan daliban da aka sace a Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Kankara da ke jahar Katsina suka iso gida.
Yaran su kimanin 340 cikin rakiyar jami'an tsaron soji da 'yan sanda, sun iso fuskokinsu cike da annuri, koda yake dukan su sun yi butu-butu da kura alamar wahala.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi waya da gwamnan jahar Katsina Aminu Bello Masari in da ya taya shi murnar samun nasarar ceto yaran.
An dai sace yaran a ranar jumu'a da dare da ta gabata a wata makarantar kwana da ke karamar hukumar Kankara a jahar ta Katsina.
Gwamnatin jahar ba ta yi cikakken bayanin yadda aka karbo yaran ba, ko da ya ke a bidiyon da kungiyar Boko Haram ta fitar da rana an ji wani mai garkuwa da yaran na fadin suna tattaunawa da gwamnati don karbar kudin fansa.
Comments