Gwamnan jahar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya umurci Malaman Jami’ar Jahar Sokoto da su koma bakin aiki ba da bata lokaci ba,bayan kwashe wata shida jami’ar na rufe sakamakon yajin aikin Kungiyar Malamn Jami’a (ASUU).
Wannan mataki na kama da bayar da umurnin nan take in da ya nuna matukar bacin ransa yadda malaman ke ci gaba da kauracewa wuraren aikinsu da zimmar bin umurnin kungiyar ta ASUU.
Ya kuma nunar da cewa babu wani hakki da malaman jami’ar Jahar Sokoto ke bin gwamnatinsa kama daga albashi ya zuwa sauran bukatu da bai yi mu su ba.
Ya bayyana cewa babu wata matsala a duniya da ta gagari tattaunawar da za ta kai ga cimma maslaha, kuma ya zama wajibi a fito da matakin da zai iya zama kandagarki ga duk wani abu da ke haifar da yajin aiki a Najeriya.
“Bai kamata ku biyewa uwar kungiya ta ASUU ba, saboda matsalolinsu ba su shafe ku ba. Kuna cutar da dalibanku ne kawai, kuma wannan biyayyar da kuke ci gaba da yi na da matukar muni da nakasu ga makomar ilmi; ina mai ba ku umurnin nan take ku koma bakin aiki ba tare da wani bata lokaci ba”, in ji gwamna Tambuwal.
Gwamnan na wadannan kalaman ne lokacin da ya karbi rahoton binciken da kwamitin da gwamnatin jahar Sokoto ta kafa karkashin jagorancin Injiniya Abdullahin Bakale, da ya gudanar da bincike dangane da tarzomar daliban Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari da ta yi sanadiyyar mutuwar wata Daliba mai suna Deborah Yakubu, har ya jawo aka rufe kwalejin.
Wannan umurnin gwamnatin jahar Sokoto na zuwa ne kwanaki kadan da kungiyar ta ASUU ta fitar da sanarwar tsawaita yajin aikin da ta ke yi da makonni hudu, lura da cewa har yanzu gwamnatin Najeriya ba ta gaji da zaman dalibai a gida ba.
An soma yajin aikin tun ranar 14 ga watan Febarairun bana, a bisa dalilin kasa cimma matsaya tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Malaman Jami’a na cika alkawurran da gwamnati ta dauka na inganta rayuwar malaman ciki har da maganar shigar da malaman cikin tsarin albashin bai daya da ka fi sani da IPPIS.
Comments