Gwamnatin jahar Sokoto ta yunkoro wajen samar da ayukkan raya gari, tun daga soma aikin Asibitin Koyarwa ta Jami'ar Jahar Sokoto da kuma Makarantar 'Yan Mata da ke garin Kasarawa galibin mazauna jahar ke ganin cewa an soma samun sauyi.
Ganin yadda aka soma wasu ayukan da aka yi shekaru ana jira. Kuma cikin sauri da kamala.
Tun lokacin zuwan gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal a 2015, galibin jama'a ke fadin albarkacin baki ganin gudanar da ayukkan kamar da wasa. To sai dai kuma, gwamnatin ta bayar da kwangiloli da suka hada da gina gadojin sama guda biyu da aka ce za a gina nan take. Kazalika da samar da filin wasa katafare da aka ambata da sauran su.
TANTABARA ta zanta da wasu mazauna yankunan da ake ayukan in da suka shaida mata cewa suna murna da samar da ci gaban idan har ya tabbata. Haka ma wasu da dama sun soma samun hanyar abin kaiwa bakin salati daga soma ayukkan, inda suka kakkafa sana'o'insu a wuraren.
A ziyarar da TANTABARA ta kai wuraren ta lura cewa a yadda aikin ginin makarantar da sibitin ke tafiya akwai yuwar kammala su a daidai lokacin da aka shata.
Wasu ra'ayoyin mazauna jahar kuma na cewa, sai gwamnatin Tambuwal ta yi da gaske domin ganin ta sha gaban gwamnatocin da suka gabace ta dangane da ayukan raya jaha. To amma kuma a cewar magoya bayan gwamnatin hakan bai rasa nasaba da karyar tattalin arzikin Najeriya sabanin a can baya, wanda ba gwamnatin Tambuwal ce kadai ta fuskanci hakan ba..
Comments