Yau an wayi gari da dogayen layuka a gidajen mai na jahar Sokoto sakamakon tsananin karancin man fetur da ake fama da shi a Najeriya fiye da wata biyu.
Galibin hanyoyin mota sun zama kusan fayau sabanin yadda aka saba, yayinda dimbin direbobi suka mamaye ciki da harabar gidajen man jahar.
Tantabara News ta samu zantawa da wasu da ke kokarin samun man da suka bayyana cewa abin ya wuce hankali. Wani direba mai suna Umar Dogon Daji ya ce, " a watannin baya muna sayen litar mai naira 165, amma yanzu akwai in da ya kai har 260".
Duk da irin wannan yanayi babu wata alamar kawo karshen wannan matsala da ta addabi kasar nan tsawon shekaru.
Wani dan bunmburutu ya sanar da wakilinmu irin yadda su ma suke shan wahala kafin su samu nasarar sayen mai a kasuwar bayan fage.
Mutumin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, " mu ma 'yan bunmburutu muna shan wuya kwarai da gaske, sai ma mun bayar da toshiyar baki sannan a ke zuba muna man".
Ya kara da cewa, "karamar robar mai da ake kira litar gaye, ita ma ta tashi daga naira 50 zuwa 150 in da ma a yau an sayar da ita naira 200".
Da dama daga wadanda Tantabara News ta samu zantawa da su, sun bayyana cewa akwai mai a gidajen sayar da shi, face dai sun lura da wata makarkashiya da dillalan man tare da masu gidajen sayar da shi ke kitsawa domin cimma wata bukata tasu.
Kwanan nan gwamnatin Najeriya ta fito karara ta bayyana cewa ta magance matsalar karancin man fetur a kasar, wadda ta taso tun a watan Febrairun bana, a dalilin dambarawar shigowa da gurbataccen mai da aka zargi wasu kamfunna da yi.
Duk da wannan yanayi, har yanzu babu wani yunkuri da gwamnatin tarayya da ta jahar Sokoto ke yi na ganin an yi wa tufka hanci.
Comments