Skip to main content

Iran Ta Sha Alwashin Murƙushe Masu Tallata Manufar Cire Hijabi

A ranar Asabar 15 ga watan Afrilun da ya gabata ne mataimakin babban lauyan ƙasar Iran ya bayyana cewa, za a gurfanar da mutanen da ke ƙarfafa mata gwiwar cire hijabi a gaban kotunan laifuka, kuma ba za su sami damar daukaka ƙara kan duk wani hukunci da aka yanke musu ba.
Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar mata da ke bijirewa dokokin sanya hijabi da Iran ta sanya, inda suke bayyana a manyan kantuna da gidajen cin abinci da shaguna da sauran wuraren taruwar jama'a.

 A cikin 'yan watannin nan wasu mata masu fafutuka sun fito fili sun yaɗa hotunan kansu a shafukan sada zumunta ba tare da lullubi ba.

Jami'an tsaron 'yan sandan Iran a ranar Asabar ɗin makon jiya, sun sanya na'urorin ɗaukar hoto a wuraren taruwar jama'a don tantancewa da kuma hukunta matan da aka gano ba su sanye da hijabi, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na Iran suka ruwaito.  

Kamfanin dillancin kabaran Reuters ya ruwaito mataimakin babban lauyan gwamnatin ƙasar, Ali Jamadi na cewa, "Duk wadda aka sama da wannan laifin take za a gurfanar da ita a gaban kotun hukunta laifuka masu alaƙa, kuma duk hukuncin da aka yanke shi ne na ƙarshe ba za a iya daukaka ƙara ba".

 Ya ƙara da cewa gwamnatin ƙasar ta yi tanadin hukunci mai tsanani ga waɗanda ke tallata manufar cire hijabi fiye da laifin cire hijabin kansa, domin yana ɗaya daga cikin bayyanannun misalai na ƙarfafa fasadi" in ji shi.

Ƙasar Iran dai na shan suka daga ƙasashen yamma da ke yi ma tsarin al'adun addini da ta runguma kallon masu tsauri kuma waɗanda duniya ta soma barin yayinsu.

Zubairu Ahmad Bashir (Kasarawa)

Ɗan jarida ne a Rediyon Tarayyar Najeriya (FRCN)

Comments

Wadanda aka fi karantawa

INEC Ta Nemi A Kama Kwamishinan Da Ya Sanar Da Sakamakon Zaɓen Adamawa

Bayan kammala wani zaman tattaunawa a jiya talata da Hukumar ta INEC ta yi a Abuja dangane da dambarwar da ta faru a jahar Adamawa.  Hukumar ta fitar da sanarwar matakin da ta ɗauka a shafinta na twitter, inda ta yi kira ga Sifetan 'yan sanda na ƙasa da ya gurfanar tare da tuhumar tsohon kwamishinan zaɓen jahar Barista Hudu Yunusa Ari. Ta kuma nemi Sakataren Gwamnatin Tarayya da ya ja hankakin hukumomin da ke da alhakin naɗa kwamishinonin zaɓe domin ɗaukar matakin da ya dace. Wannan dambarwar ta soma ne tun daga ranar Lahadi lokacin da kwamishinan zaɓen ya ayyana A'ishatu Ɗahiru Binani a matsayin wadda aka zaɓa gwamnar jahar Adamawa gabanin a kammala tattara sakamakon zabe.

Da Dumi Dumi An Ceto Yaran Da Aka Sace A Katsina

Sakataren gwamnatin jahar Katsina Alhaji Mustapha Inuwa ya fitar da sanarwar cewa an samu nasarar ceto daliban nan da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su daga makarantar kwanan ta Kimiyya da ke Kankara a jahar Katsina. Ya ce an ceto yaran su 340, kuma yanzu haka suna kan hanyarsu ta isowa jahar daga Tsafen jahar Zamfara. Ana sa ran gobe jumu'a za su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin daga bisani a sada su da iyayensu. Sauran bayani zai zo nan gaba.

Takalman Fir'auna

Takalman Zinariya na Fir'auna Tutankhamun, na daula ta 18 wadda ya yi mulki shekaru 1,300 kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Yanzu haka waɗannan takalman na nan a Gidan Adana kayan Tarihi na Masarautar Alƙahira da ke Misira 📷 Saliadeen Sicey