Skip to main content

Halin Da Ake Ciki Kan Yunƙurin Juyin Mulki A Sudan

Jami'an Ɗaukin Gaggawa don Tallafa ma Tsaro a Sudan na Rapid Support Forces (RSF) a yau asabar sun ce sun ƙwace iko da fadar shugaban ƙasa da gidan hafsan hafsoshin soji da babban filin jirgin sauka da tashin jiragen sama a birnin Khartoum a wani yunƙurin juyin mulki da aka yi a lokacin da rikici ya ɓarke tsananinsu da sojoji.
Rundunar ta RSF wacce ta zargi sojojin da fara kai mata hari, ta kuma ce sun ƙwace tashoshin jiragen sama a arewacin garin Merowe da kuma El-Obeid a yammacin ƙasar.

Rundunar sojin saman Sudan na ci gaba da fatattakar mayaƙan RSF, a cewar wata sanarwa rundunar.  

Wasu gidajen talabijin sun nuna wani jirgin soji a sararin samaniyar birnin Khartoum, amma Tantabara News ba ta tabbatar da sahihancin labarin.

Rahotanni da ke shigo muna yanzu haka na bayyana cewa ana iya jin ƙarar harbe-harbe a sassa da dama na birnin Khartoum inda wasu shaidun gani da ido da ke bayar da rahoton harbe-harbe a garuruwan da ke makwabtaka da su, lamarin da ya sa ake fargabar ɓarkewar wani sabon rikici.

Comments