Skip to main content

Kalubalen Tsaro Da Canza Shekar Kwamishinan Tsaron Jahar Sokoto

 

A daidai lokacin da matsalar tsaro ke ʙara ta’azzara a jahar Sokoto, kwamishinan tsaron jahar Kanal Garba Moyi (mai ritaya) ya bayar da sanarwar aje muʙaminsa tare da ficewa daga jam’iyyar jam’iyar PDP mai mulkin jahar.

A cewar tsohon kwamishinan tsaron, ā€œakwai gaggan matsaloli da suka taka rawa wajen ficewarsa daga jam’iyayar, da suka haɗa da sakacin gwamnan jahar, Aminu Waziri Tambuwal na watsi da dukan  shawarwarin da ake ba shi da suka shafi tsaro; kazalika da rashin sauraren ʙorafe- ʙorafen dangane da ci gaban jahar a fannoni da damaā€.

A ranar alhamis da ta gabata dai wasu ā€˜yan bindiga suka kai wani hari a garin Chakai da ke ʘaramar Hukumar Mulki ta Tambuwal, wadda ita ce mahaifar gwamnan jahar, in da suka sace mutum goma sha bakwai ciki har da mata da ʙananan yara, tare da neman diyyar naira miliyan takwas da dubu ɗari biyar. Kazalika, sun fitar da sanarwar shirin hallaka mutanen daga gobe talata, muddin ā€˜yan uwan wadanda ake garkuwa da sun ba su aika mu su kuɗin fansar da suka nema tun da farko ba.

Wani mai suna Alhaji Muhammadu Ɗanyaya, da aka sace matarsa da kuma ā€˜yarsa mai takaba, ya shaidawa Tantabara cewa, suna cikin babban ʙalubalen tsaro kuma babu wata huɓɓasa daga ɓangaren gwamnatin jahar Sokoto wajen kawo ʙarshen matsalar;ga shi  kuma gwamnati ta haramta ayukkan ā€˜yan sa kai ballantana su ji ʙwarin guiwar kare kan su. Ya kuma bayyana rashin tartibiyar hanyar da za su bi wajen samo kuɗin fansar da mayaʙan suka nema, ā€œa halin da ake ciki yanzu, ba mu da kuɗin da ā€˜yan bindigar suka nema, amma dai muna nan muna ʙoʙarin ganin mun sai da gona, an sai da shanu da ā€˜yan awaki, har ma da kaji dai mata na ta ʙoʙari mai kawo taro sisi na yi, a na ta ʙoʙarin yadda za a haɗa kuɗin, kuma ga shi kudin dai sun buwaya; su kuma suna ta cewa ko ta yaya dole sai a biya kuɗin fansar kafin su sako muna mutanenmu ko su hallaka su daga gobe talataā€.

Tantabara ta yi ʙoʙarin ji daga bangaren gwamnatin jahar Sokoto kan wannan lamari amma kawo haɗa wannan rahoto babu wani martani daga mahunkutan.

Jahar Sokoto na cikin sahun gaba a jerin jahohin arewa maso yamma da yanzu haka ke fuskantar hare-haren ā€˜yan bindiga; in da kwanan nan ā€˜yan ta’adda suka kai farmaki a garuruwan Tureta da Gidan Dilo da ke yankin Nakasari da Illela da kuma garin Tambuwal.

Kodayake wasu na danganta saukar kwamishinan tsaron jahar ta Sokoto  a matsayin siyasa, wasu masana  na ganin lamarin ya bar baya da ʙura, in da su ke ganin wata babbar koma baya ce a daidai lokacin da ake neman yi ma tufka hanci a fannin na tsaro.

 

 

 


Comments