Skip to main content

Abduljabbari Ya Ce Idan An Ba Shi Sarari Zai Tuba

 Abduljabbari ya koka a kan yadda mukabalar ke tafiya, duk da ya kasa amsa muhimman tambayoyin da aka yi masa.
Ya ce mintina 10 da aka ba shi don ya amsa tambayoyin da suka shafi cin zarafin Annabi (s.a.w.) ba za su isa ya kwance littafai kusan 500 da ya zo da su ba.
An tambai shi ko a wane hadisi aka kira annabi bunsuru ko arne?
Ya ce idan an ba shi karin lokaci zai binciko hadisan ya zo da su amma yanzu an kure shi ba cikin shiri yake ba, kuma gaba daya a cewar sa, babu gaskiya a mukabalar. Ya ce yana son ne ya tsamo mutane daga halakar da ke sa suna yin ridda sakamako rudanin hadisan.
Kasancewar wannan kasawa ya sa daya daga Malaman da ke zurara masa tambayoyi Malam Abubakar Madatai ya neme shi da ya tuba ya tabbatar da kuskuren da ya yi.
Amma Abduljabbar ya ce ta ya zai tuba a wajen wannan muƙabala, a gaban kowa da kowa, ba tare da ba shi karin lokaci don haduwa ta gaba ba, sannan a ba shi karin wasu hujjoji da suka fi nasa.
 Da ya ki tuba, malamin na bangaren Tijjaniya ya kuma nemi ya yi bayani a wane hadisi aka ambaci cewa annabi (s.a.w.) ya sha giya a lokacin aurensa Nana Khadija, da kuma tambayar da Malam Mahmud Hotoro Kano ya sake yi masa na karin haske akan kiran annabi da bamaguje da aka yi,  dukan su dai ya ce ba a fahimce shi ba kuma ya na so a sake saka wata sabuwar rana don ya shirya.

Comments