Skip to main content

'Yan Takarar Shugaban Kasa Sun Fara Janye Ma Bola Tinubu

Kawo yanzu dai akwai masu neman mukamin shugaban kasa da suka fito kafin fara jefa kuri'a suka bayyana cewa sun janye takararsu kuma sun marawa tsohon gwamnan jahar Legas Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Daga cikin su akwai gwamnan jahar Jigawa Muhammadu Badaru Abubakar da Fayemi Kayode da Ajayi Boroffice da tsohon kakakin majilasar wakilai Dimeji Bokole da kuma Gidein Akpabio.
Amma Pasto Tunde Bakari ya bayyana cewa shi kam ba zai jaye ma kowa da ga cikin 'yan takara ba, kasancewar "ba su da kyakkyawar manufar gina kasa face rusa ta", in ji shi.
Akwai 'yan takara da dama da ya zu haka su ke jiran a fara kada kuri'a da suka hada da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da sanata Ahmed Yariman Bakura da gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello da Rotimi Amechi da sauran su.

Zamu kawo mu ku karin labari nan gaba.

Comments

Wadanda aka fi karantawa

INEC Ta Nemi A Kama Kwamishinan Da Ya Sanar Da Sakamakon Zaɓen Adamawa

Bayan kammala wani zaman tattaunawa a jiya talata da Hukumar ta INEC ta yi a Abuja dangane da dambarwar da ta faru a jahar Adamawa.  Hukumar ta fitar da sanarwar matakin da ta ɗauka a shafinta na twitter, inda ta yi kira ga Sifetan 'yan sanda na ƙasa da ya gurfanar tare da tuhumar tsohon kwamishinan zaɓen jahar Barista Hudu Yunusa Ari. Ta kuma nemi Sakataren Gwamnatin Tarayya da ya ja hankakin hukumomin da ke da alhakin naɗa kwamishinonin zaɓe domin ɗaukar matakin da ya dace. Wannan dambarwar ta soma ne tun daga ranar Lahadi lokacin da kwamishinan zaɓen ya ayyana A'ishatu Ɗahiru Binani a matsayin wadda aka zaɓa gwamnar jahar Adamawa gabanin a kammala tattara sakamakon zabe.

Da Dumi Dumi An Ceto Yaran Da Aka Sace A Katsina

Sakataren gwamnatin jahar Katsina Alhaji Mustapha Inuwa ya fitar da sanarwar cewa an samu nasarar ceto daliban nan da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su daga makarantar kwanan ta Kimiyya da ke Kankara a jahar Katsina. Ya ce an ceto yaran su 340, kuma yanzu haka suna kan hanyarsu ta isowa jahar daga Tsafen jahar Zamfara. Ana sa ran gobe jumu'a za su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin daga bisani a sada su da iyayensu. Sauran bayani zai zo nan gaba.

Takalman Fir'auna

Takalman Zinariya na Fir'auna Tutankhamun, na daula ta 18 wadda ya yi mulki shekaru 1,300 kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Yanzu haka waɗannan takalman na nan a Gidan Adana kayan Tarihi na Masarautar Alƙahira da ke Misira 📷 Saliadeen Sicey