A wani abinda ba saban ba, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana Sanata Aisha Dahiru, wacce aka fi sani da Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen gwamnan jahar Adamawa.
Kwamishinan zaɓen jahar Adamawa, Farfesa Hudu Yunus Ari, ya ayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen ana tsakiyar tattara sakamakon zaɓen.
An bayyana sakamako daga ƙananan hukumomi 10 cikin 20 yayin da aka dage ci gaba da bayyana sakamakon zaɓen har zuwa karfe 11 na safe.
Sai dai Ari ya sanar da sakamakon ƙarshe awa ɗaya kafin lokacin da aka tsara.
Gwamnan jahar Ahmadu Fintiri na jam'iyyar PDP ne ke kan gaba kafin a bayyana hakan.
Wasu magoya bayan jam’iyyar PDP a zauren sun nuna rashin amincewarsu da dalilin da ya sa kwamishinan zaɓe ya sanar da sakamakon maimakon baturen tattara sakamakon zaɓe a al'adance.
Comments