Skip to main content

An Ɗaure Wani Ɗan Jaridar Rasha Kan Sukar Putin

Wata kotu a kasar Rasha ta yankewa ɗan jarida hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari bisa zargin sa da yin kira da a hambarar da gwamnatin shugaba Vladimir Putin bayan mamayar da ya yi ma ƙasar Ukraine a bara.
Shafin yanar gizo na ‘yan shafin yanar gizo na jami'an tsaron 'yan sanda na OVD Info  ya ruwaito ranar Juma’a cewa, an kama Kirill Akimov, mai shekaru 52 a watan Yuni, bisa zargin yin kiraye-kirayen da ka iya kai wa ga tashin hankali yayin gabatar da shiri a wani gidan rediyo a ranar 14 ga Maris, 2022.

 Akimov, wanda ya fito daga Jamhuriyar Mordovia ta tsakiyar Rasha, mai tazarar kilomita 400 gabas da birnin Moscow.

Kotun soji da ke Yekaterinburg a ranar Laraba ta samu Akimov da laifuffuka biyu na ingiza jama'a su yi bore da kuma aikata ta’addanci, a cewar wata kotu.

Comments