Skip to main content

Burtaniya Ta Kakabawa Bankunan Rasha da Mahukuntan Kasar Takunkumin Tattalin Arziki Mafi Girma A Tarihi

Getty images
Firaministan Burtaniya, Boris Johnson ya sanar da sakawa Rasha takunkumi mafi tsanani a bangaren tattalin arziki da Rasha ta taba gani, tun bayan da ta mamaye Ukraine. Da yake magana a zauren majalisar, firaministan ya ce za a daskarar da duk wasu manyan bankunan kasar Rasha da kuma cire su daga tsarin kudi na Burtaniya. 
Har ila yau, za a dakatar da kamfanin jiragen saman Rasha na Aeroflot sauka a kasar Birtaniya. Mista Johnson ya shaidawa majalisar dokokin kasar a yammacin ranar almais din makon nan cewa, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin "mai cin zali ne mai zubar da jini, don haka zai yabawa aya zakinta".

Comments