'Yan majalisar wakilan Amurka yanzu haka sun soma jefa kuri'ar tsige shugaba Donald J. Trump.
Sun soma kada kuri'ar ne bayan kammala muhawarar da ta bada damar ci gaba da daukar mataki na gaba, wanda shi ne kada kuri'ar amincewa ko akasin haka.
An dai baza dubban jami'an tsaron soji a ko'ina ciki da harabar majalisar dokoki ta Capitol Hill don shirin ko ta kwana.
Bayan kammala jefa kuri'ar daga baya za a turawa majalisar dattijai don daukan mataki na gaba da zai iya kai ga tsige shi ko sabanin haka.
Idan har haka ta tabbata zai zama kenan Trump shi ne shugaban Amurka na farko a tarihi da aka tsige har sau biyu.
Wannan sabon matakin na da nasaba da jawaban shugaban a makon jiya, da 'yan majalisar suka ce sun kai ga tunzura magoya bayansa har suka kai wa majalisar hari da yayi sanadiyyar mutuwar mutum biyar, ciki kuwa har da jami'in dan sanda da ke kare masu zanga-zangar daga kutsa kai ginin majalisar.
Comments