A daren jiya Talata ne wasu yan bindiga sukayi dirar mikiya a wani kauye mai suna Chacho da ke karamar hukumar mulki ta Wurno da ke jahar Sokoto.
Rahotanni na cewa maharan sun kai wa wani Dan kasuwa mai suna Alhaji Jamilu samame ne da niyyar hallaka shi, amma da hakansu ba ta cimma ruwa ba suka yi awon gaba da mahaifinsa hadi da matarsa da kuma harbin kanensa, tare da karbar kudin da suke mallakarsa ne kimanin naira dubu dari shida da sittin.
Maharan sun kuma harbe wani dan banga har lahira, mai suna Malam Rabi'u.
Wannan lamarin yawitar hare-hare a jahar Sokoto na neman gagarar kundila, domin kwana daya kawai kafin wannan harin wasu 'yan bindiga sun kai farmaki a wani gari da ke karamar hukumar ta Wurno da suka karbi kudi naira miliyan daya daga hannun wani dan kasuwa kafin daga bisani jami'an tsaro su yi nasarar kama biyar daga cikin su.
Comments