Skip to main content

Da Dumi Dumi - An Tsige Shugaba Trump


Majalisar wakilan Amurka sun samu yawan kuri'un da za su kai ga tsige shugaba Donald Trump.
Wannan ya tabbatar da shi a matsayin shugaban Amurka na farko da ka tsige har sau biyu. Kuma wannan zai hana ma sa sake rike kowane irin mukamin siyasar kasar nan gaba da kuma bada damar gurfanar da shi don fuskantar tuhuma a gaban kotu.
Ga jerin shuwagabannin Amurka da aka taba tsigewa:
 A shekarar 1868 an tsige shugaban Amurka Andrew Johnson, 
Sai kuma shugaba Bill Clinton da aka taba tsigewa a 1998.
Bayan sa kuma sai shugaban Amurka mai barin gado Donald J. Trump shi kuma  a 2019. Bayan nan kuma yau 13 ga watan Janairun 2021 an sake tsige tsohon shugaban a karo na biyu.

Comments