'Yan majalisar dokokin Amurka sun soma wani zama na musamman yanzu haka, don shirin tsige shugaba Donald Trump, ana sauran kwanaki 9 kacal a rantsar da zababben shugaban kasar Joe Biden.
Kakakin majalisar dattawan kasar Nancy Pelosi a wata hira da tashar talabijin ta NBC, ta ce, "Mista Trump zai fuskanci zahiri ta hanyar girbar abinda ya shuka". Ta ce za su nemi mataimakinsa Mike Pence ya aminta tare da sa hannu akan kudurin dokar da zai nuna amincewa da cewa shugaba Trump bai dace ya shugabanci kasar ba, ko kuma idan har hakan ta ci tura, su soma jefa kuri'ar amincewa da tsige shi a tsakiyar makon nan.
Idan har hakan ta tabbata wannan ya nuna Trump ne shugaban Amurka na farko da aka taba tsigewa har sau biyu. Kuma hakan zai bata ma sa suna da makomar siyasa nan gaba.
Masana shari'a na ganin bayan tsige shi, zai iya fuskantar tuhuma akan zargin ingiza magoya bayansa su kai hari da zanga-zanga a majalisar dokokin kasar, domin hana amincewa da zaben Joe Biden, abinda kuma shi ne irin sa na farko a tarihin kasar.
Comments