An rantsar da shugaban Amurka na 46 Joe R. Biden tare da mataimakiyarsa Kamala Harris.
Shugaba Biden ya nemi goyon bayan Amurkawa wajen samar da hadin kan kasa.
"Ina neman hadin kan ku wajen ci gaba da ginin dimukuradiyarmu mai shekaru fiye da dari biyu ta ci gaba", in ji Biden.
Ya kara da cewa, "Fatan da na sa gaba idan na shiga ofis, shine tabbatar da Amurka ta dore a yadda a ka santa, da inganta huldar dangantaka tsakanimu da waje, yaki da korona hadi da tabbatar da Amurka ta ci gaba da zama dunkulalliyar kasa".
Shahararriyar mawakiyar nan, Lady Gaga ce ta rera taken kasar, haka ma mawakiya Jennifer Lopez ta nishandantar da mahalarta bukin.
An dai gudanar da bukin cikin tsauraran matakan tsaro.
Tun da safiyar yau tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya bar fadar White House cikin wani jirgi mai saukar ungulu in da ya nufi jahar Florida. A can zai yi jawabin shirin kafa sabuwar jam'iyarsa da ya ce za ta samarwa Amurka makoma kasancewar manyan shugabannin jam'iyar Republican na ta nesanta kan su da shi.
Comments