Malamin ya sanar da cewa maharan da suka sace daliban wata Makaranta da ke Kagaran jahar Naija, sun kira shi domin ya nemo gwamnati a tattauna yadda za a saki yaran.
Shak Ahamd Gumi ya ce, shi kan sa bai san in da maharan ke fakewa ba, amma dai ya samu tattaunawa ta waya da shugaban 'yan fashin da suka addabi yankunan arewacin Najeriya, mai suna Dogo Gide, in da ya sanar da malamin alkawarin da suka dauka na tattaunawa da gwamnati.
To amma kuma har yanzu bangaren gwanatin tarayya da ma jahohi ba su ce uffan ba kan wannan batu. Duk dai kokarin da jami'an tsaro na gano in da wadannan mahara ke fakewa a dazuka ya ci tura, amma a galibin lokuta Shak Ahmad Gumi ya sha kutsa kai a dazuka da zimmar ilmantar da su da kuma nan shiga tsakani don neman sulhu.
Sai dai a duk wannan kokari da Ahmad Gumi ya nuna yana yi hare-haren 'yan bindiga sai karuwa suke, inda wannan kwashe dalibai a makarantun kwana shi ne na hudu baya ga makarantar Kankarar jahar Katsina kimanin watanni biyu da suka gabata, in da wasu mahara suka yi garjuwa da dalibai 344 a dajin Tsafe ta jahar Zamfara.
Masana na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan wannan lamari mai daure kai, in da ko jiya an jiyo fitaccen lauyan nan Barista Bulama Bukarti na shedawa BBC Hausa cewa, akwai lauje cikin nadi a yadda wadannan mahara suka mayar da wannan garkuwa da jama'a a matsayin sana'a.
Kawo yanzu dai ba a san wane irin sulhu maharan ke nema a yi ba alhali suna rike da yaran.
Amma dai malamin ya ce maharan sun koka a kan yadda jami'an tsaro ke addabar su idan sun shigo gari. Kazalika, ana yawan kai mu su hari abinda a cewarsu muddin ba daina ba to ba za a zauna lafiya ba; sai dai bangaren jami'an tsaron Najeriya ba su bayyana ko za su daina kaiwa mayakan hari ba.
A jiya dai ne ministan tsaron Najeriya Bashir Magashi ya fito fili ya bayyana cewa bai dace jama'a su dinga gudun maharan ba, a maimakon haka ya kamata su yaki 'yan bindigar, kalaman da suka jawo cece-kuce tsakanin 'yan Najeriya da ke cewa akwai alamun gwamnatin Najeriya ta kasa a bangaren tsaro.
Comments