Skip to main content

TAURARUWA MAI WUTSIYA... GANDUJE KO ABDULJABBARI?

RA'AYI:
Dambarwar da ta dabaibaye batun nan na dakatar da Abduljabbar Nasiru Kabara a jahar Kano na ta jan hankalin al'umma a kwanan nan. Lamarin ya ja ra'ayin masana da masu sharhi na ta tofa albarkacin bakinsu kan batun. Wannan ya sa jaridar Tantabara News ta yi tsokaci akan yadda masana da tarihi ya hango makomar irin wadannan mutane.
A ranar larabar makon jiya ne gwamnatin jahar Kano ta dauki matakin rufe masallacin da malamin ke da'awa da aka fi sani da suna As-habul Kahf da ke takiyar birnin Kano. Haka ma gwamnatin ta hana ma sa yin da'awar tare da yi ma sa wani abu mai kama da daurin talala; da ta bayyana da cewa kandagarki ne ga irin matakan da aka lura ya na dauka na hargitsa jama'a tare da boyayyar manufa mai jirwaye kama da wanka.
  Wanene Abduljabbar Nasir Kabara?
 Abduljabbari dai matashin malami ne mai dimbin magoya baya, mai son daukaka da suna a kafofin sada zumunta na zamani da kafar sadarwa ta YouTube mai kare mashabar Shi'a akaikaice ta karkashin inuwar darikar Kadiriyya.
Mahaifinsa, Shaikh Nasiru Kabara, wanda shi ne jagoran darikar Kadiriyya a Kano da yayi suna a lokacinsa, ko da ya ke shi ma ya samu takon saka da wasu malamai ma su neman a hargitsa, irin su Sheikh Bala Kalarawi Kano. An dai bayyana mahaifin Abduljabbari a matsayin mutum mai bambancin ra'ayi da saukin kai ba irin yadda shi dansa ya ke ba.
Me Ya Jawo Aka Dakatar Da Shi Wa'azi?
To amma kuma, wannan matakin da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya dauka, a ganin wasu bai rasa nasaba da siyasa; wasu kuma na ganin kin darikar ne.
A ra'ayin Muhammad Sidk Qaddam Isah mazauni Hadaddiyar Daular Larabawa, kuma mai sharhi akan al'amurran gabas ta tsakiya da ma sauran duniya, ba haka ba ne. Ya kalli wannan mataki a matsayi kyakkyawa, a bisa hujjojin da ya za zayyano a mukalar da ya wallafa a shafinsa na bulog, a harshen turanci da yayi ma take: Kano Kogo Cleric, wato Malamin Kogo na Jahar Kano. Kogo anan ya samo asali ne daga sunan masallacinsa, As-habul Kahf wanda ke nufin mutanen kogo.
Muhammad Qaddam ya kara da cewa, "Malamin mai karancin haddar Al-kur'ani da karancin ilmin tajwidinsa.....na kokarin kawo ko-kwanto ga hadisan manzon tsira tare da kokarin fassara hadisan ta gundarin zahirinsu a maimakon sakonsu. Yana amfani da gurgun ilmin harshen larabcin da ke da kasawa, wajen bayyana ma'anar (hadisan) da za ta kai ga karshe ya karyata su, ya watsar da su".
"Ya kan bin salon Mu'utizilawa masu akidar Shi'a da ke suka ga hadisai tare da bayyana raddin da ba a gina ga hujja ba. A maimakon (tsarin da aka sani) shi ya kan ce fassarar da yayi mu su a bisa ra'ayinsa ne da ilminsa ya ke kawo tartibin yadda sahabbai da na bayansu suka bayyana addinin musulunci a daruruwan shekaru".
     (mohammadsidq.blogspot.com
Haka ma jaridar Daily Trust ta ranar Jumu'a 5/2/2021 ta buga sharhin).
Gwamna Ganduje dai ya bayyana dalilin cewa akwai alamar Abduljabbari na kira ne da a yi tawaye, da kisan kai da nuna kangara wa gwamnati a dukan wa'azojinsa. Misalin hakan shi ne wani kira da ya ke na cewa duk wanda ya shiga wajen da ya ke wa'azi don ya farma (kama) sa, to magoya bayansa su "kama wannan mutumin su yanka shi, su yanka shi, su yanka shi"!!
Wanda a cewar gwamnati yana nufin jami'a tsaro.
Ganduje ya bayyana hakan a kafafen watsa labarai cewa, bai dauki matakin dakatar da shi daga wa'azi tare da rufe masallacin haka siddam ba, sai da ya samu rahotanni da shawarwari daga muhimman mutane.
Wasu na ganin akwai siyasa a ciki lura da yadda dangantaka ta yi tsami tsakanin gwamna Abdullahi Umar Ganduje da tubabben sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II, wanda shi sarkin Kanon na goyon bayan gidan su marigayi Nasiru Kabara, in da nan ne Abduljabbari ya fito.
Galibin jama'a na ganin daukan matakin ya dace, ganin irin yadda a hakan Maitatsine ya fara a Kanon; haka shugaban kungoliyar Boko Haram na farko Muhammad Yusuf ya fara. Kuma shi ma Muhammad Yusuf yayi zaman mukabila da manyan malamai irin su marigayi Shaik Jafar Adam Kano da marigayi Shaik Albani Zariya da Shaik Isah Ali Pantami da sauran su, akan cewa da'awar da ya ke ta sabawa shari'a wanda sai yanzu ne jama'a suka gasgata su alhali an makara.
A kan wannan aka bayyana Abduljabbari Nasir Kabara a matsayin mai neman suna da son mamaye manyan malaman hadisi ta hanyar tara magoya baya da karkatar da su don neman dagawa a sama.
Sai dai a ra'ayin magoya bayansa, shi mutim ne da ya zo da niyyar tsarkake tsarin koyarwar addini da yadda ake wa'azi ana jingina wasu hadisai ga annabi mai tsira da amincin Allah.
Wani abu da ake danganta Abduljabbar da shi, bai wuce goyon bayan akidar Shi'a a kaikaice ba. Shi da kan sa ya karyata hakan amma ya bayyana cewa ya "rantse da Allah ko a haka Shi'a ta fi sunna sau dari", sai dai bai bayyana wace sunnar ba.
A wasu daga bidiyoyinsa ya taba cewa ko da Ganduje ya aiko a kashe shi, a harbe shi to ba shi aka haifa ba "Annabi (S.A.W.) aka harba!!!" Irin wadannan magangannu sun jawo an kasa gane in da ya dosa, kuma mutane hatta magoya bayan darkar ta Tijjaniya suka soma tunanin ta natsu da zargin lamarin kama da tauraruwa mai wutsiya, da ma su iya magana suka ce ganin ta ba alhairi ba!.
Koma dai menene, lokaci zai tabbatar da shi. Kamar yadda wasu ke cewa da wuya gwamna Ganduje bai kare da shi ba, kamar yadda gwamnan jahar Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i ya kare da Elzakzaki.
WANNAN RA'AYI NE NA JARIDAR TANTABARA NEWS, KUMA BAI DA MANUFAR SUKA KO BATANCI GA KOWA.

Comments