Kwana biyu kafin ta gudanar da babban zabenta na kasa, jam'iyyar APC ta sake tsunduma wata sabuwar turka-turka game da makomar wanda za a zaba matsayin sabon shugabanta.
A wata hira da BBC Hausa, gwamnan jahar Kebbi Abubakar Atiku Bagudo, wanda kuma shi ne shugaban gwamnonin APC na kasa ya ce yanzu haka sun kasa cimma matsaya akan wanda zai zama shugaban jam'iyyar a ranar asabar mai zuwa. Bagudo ya kara da cewa sun gana da shugaba Muhammadu Buhari akan samar da matsaya, amma kuma sun lura cewa da wuya idan ba zabe za a gudanar ba a maimakon samar da maslaha.
Da aka tambai shi ba ya ganin samar da maslaha tamkar an tilastawa wani ne bin abinda ba ya so, shugabana kungiyar gwamnonin ya ce zai yuwu a sulhunta amma idan hakan ta gagara za a bi hanyar da za ta kawo mafita. Sai dai bai yi cikakken bayani akan wace hanya ce da za a bi idan har an kasa yin sulhu tsakanin 'yan takara.
Ga alama wannan na nuna irin yadda jam'iyyar za ta fuskanci kalubale gabanin ko bayan gudanar da babban zaben.
A ranar talatar makon nan tsohon gwamnan jahar Zamfara, Abdul'aziz Yari Abubakar shi ma ya fito ya nuna bukatar tsayawa takarar neman muƙamin shugaban jam'iyyar APC.
Comments