Skip to main content

Kasar Isra'ila Na Kaiwa 'Yan Jarida Hari

 GAZA: Wani hari ta sama da Isra’ila ta kai ya lalata wani dogon gini a birnin Gaza wanda ke dauke da ofisoshin kamfanin dillacin labarai na Associated Press da sauran kafafen yada labarai a yau Asabar, wannan farmakin sojin ya zo ne kwatsam ba tare da yin gargadi ga mazauna ginin ba, matakin da sojoji suka dauka na yin shiru a yayin fafatawarsu da kungiyar Hamas.
Harin ta sama ya zo ne kasa da sa'a guda bayan da sojojin suka umarci mutane su fice daga ginin, wanda kuma ya hada da Al-Jazeera, da sauran ofisoshi da gidajen jama'a. Karfin harin ya ruguje daukacin ginin mai hawa 12, qanda ya haddasa turnukewar ƙura.  Babu wani bayani akan dalilin da ya sa aka kai harin.
 
Wannan sabon farmakin na zuwa ne sa’o’i bayan da wani harin sama da Isra’ila ta kai a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke da yawan jama’a a garin na Gaza da ya kashe Falasdinawa akalla 10 'yan asalin dangi daya, wadanda galibinsu kananan yara ne, a wani hari mafi muni da aka kai a rikicin da ke wakana yanzu.  
Duka bangarorin biyu sun matsa lamba don cin nasara yayin da kokarin tsagaita wuta ya gagara. 
Barkewar rikici na baya-bayan nan ya fara ne daga Kudus kuma ya bazu a yankin, inda arangamar yahudawa da Larabawa da tarzoma a garuruwa masu hade da Isra’ila ke ci gaba da yaduwa. 
Haka nan kuma an yi zanga-zangar Falasdinawa da yawa a ranar Juma’a da yau din nan a Yammacin Gabar Kogin Jodan, yankin da sojojin Isra’ila suka harbe kimanin Falasdinawa 11.

Comments

Wadanda aka fi karantawa

INEC Ta Nemi A Kama Kwamishinan Da Ya Sanar Da Sakamakon Zaɓen Adamawa

Bayan kammala wani zaman tattaunawa a jiya talata da Hukumar ta INEC ta yi a Abuja dangane da dambarwar da ta faru a jahar Adamawa.  Hukumar ta fitar da sanarwar matakin da ta ɗauka a shafinta na twitter, inda ta yi kira ga Sifetan 'yan sanda na ƙasa da ya gurfanar tare da tuhumar tsohon kwamishinan zaɓen jahar Barista Hudu Yunusa Ari. Ta kuma nemi Sakataren Gwamnatin Tarayya da ya ja hankakin hukumomin da ke da alhakin naɗa kwamishinonin zaɓe domin ɗaukar matakin da ya dace. Wannan dambarwar ta soma ne tun daga ranar Lahadi lokacin da kwamishinan zaɓen ya ayyana A'ishatu Ɗahiru Binani a matsayin wadda aka zaɓa gwamnar jahar Adamawa gabanin a kammala tattara sakamakon zabe.

Da Dumi Dumi An Ceto Yaran Da Aka Sace A Katsina

Sakataren gwamnatin jahar Katsina Alhaji Mustapha Inuwa ya fitar da sanarwar cewa an samu nasarar ceto daliban nan da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su daga makarantar kwanan ta Kimiyya da ke Kankara a jahar Katsina. Ya ce an ceto yaran su 340, kuma yanzu haka suna kan hanyarsu ta isowa jahar daga Tsafen jahar Zamfara. Ana sa ran gobe jumu'a za su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin daga bisani a sada su da iyayensu. Sauran bayani zai zo nan gaba.

Takalman Fir'auna

Takalman Zinariya na Fir'auna Tutankhamun, na daula ta 18 wadda ya yi mulki shekaru 1,300 kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Yanzu haka waɗannan takalman na nan a Gidan Adana kayan Tarihi na Masarautar Alƙahira da ke Misira 📷 Saliadeen Sicey