Shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya soki kasar Amurka akan irin rawar da dala ke takawa a tattalin arzikin duniya tare da yin kakkausar suka ga asusun lamuni na duniya na IMF.
"Me ya sa kowace ƙasa za a danganta da dala don kasuwanci? Wanene ya yanke shawarar dala za ta zama kuɗin duniya?"
Ya ƙara da cewa me yasa banki kamar bankin BRICS ba zai iya samun kuɗin da zai gudanar da hulɗar kasuwanci tsakanin Brazil da Chana ba, da ma sauran ƙasashen duniya?
Ya ce yana mamakin yadda ƙasashe cike da rauni su ke bin sawun amfani da dala wajen gudanar da kasuwanci alhali suna iya hakan da kuɗaɗensu.
A wata ganawa tsakanin sa da shugaban Chana Xi Jinping, da kuma ya wallafa a shafinsa na twitter ,shugaban na Brazil ya ce, " a yanzu Brazil ta dawo, lokaci ya wuce da a ka daina jin duriyar Brazil, a yanzu kam mun dawo".
Lula ya kuma yi suka mai ƙarfi kan yadda Bankin bayanar da lamuni na duniya IMF, ke kassara tattalin arzikin ƙasashen duniya yana mai nuni da zargin da ake yi wa IMF na tsarawa kasashen yadda za su tafiyar da tattalin arzikinsu, kamar dai yadda ke faruwa a Brazil da Argentina da sauran su.
A na yi ma wannan sabon mataki da ƙasashen suka ɗauka na amfani da kuɗaɗensu a matsayin tawaye ga ƙasar Amurka da dangoginta, na kauce wa amfani da dala a wajen auna mizanin tattalin arziki da gudanar da hada-hadar kasuwanci tsakanin ƙasa da ƙasa.
Comments