Har yanzu ana ci gaba da jefa kuri'a kuma kimanin jaha 14 ne suka kaɗa ƙuri'unsu a zaben fidda gwani na APC da ke gudana a Dandalin Eagles da ke Abuja.
Wadannan jahohin su ne Abia da Kano da Katsina da Adamawa da Delta da Cross River da Osun da Ogun da Borno da Neja da Binuwai da sauran su.
Zuwa tsakar daren jiya an dan samu tsaiko na awa guda kasancewar an samu wasu daliget da kuri'un bogi, wanda aka dakatar da zaben kafin daga baya a ka ci gaba.
Comments