Skip to main content

Gwamnatin Tarayya Ta Shawarci Ɗalibbai Su Maka ASUU Kotu

Kasancewar zaman tattauna tsakanin Ƙungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU) da gwamnatin tarayya an tashi dutse a hannun riga, hakan ya fusata gwamnatin tarayyar Najeriya, in da aka jiyo Ministan Ilmin ƙasar, Malam Adamu Adamu na shawartar ɗaliban jami'ar da ke zaman jira a gida na su maka ƙungiyar a kotu.
Ministan ya ce dukan alhakin ɓatawa ɗaliban lokaci ya rataye a wuyan malaman jami'a, kuma ya zama wajibi su biya ɗaliban diyya. Ya kuma ce gwamnatin tarayya za ta saka ƙafar wando guda da malaman ta hanyar ƙin biyansu albashin watannin da suka kwashe ba tare da aiki ba. Wasu daga cikin malaman jami'ar sun fara mayar da martani kan wannan matsaya ta gwamnatin tarayya. Dakta Mansur Isah Buhar, na Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, "Na amice ɗari bisa ɗari cewa adalci ne kada a biya membobin ASUU albashinsu na tsawo wata shida da suka kwashe suna yajin aiki, saboda kuwa ai ba su yi aikin da ya dace a ce sun yi a waɗannan watannin ba. Haka kuma na amince ɗari bisa ɗari cewa adalci ne su ma malaman su kauce wa aikin (koyarwa da makin jarabawa da kuma duba ɗalibai) da ba a biya ba a watannin Febarairu zuwa Agusta, sai a ɗora daga in da aka tsaya a lokacin da aka dawo karatu daidai da kalandar karatun jami'oinsu. Idan babu aiki babu albashi; idan babu albashi, to babu aiki." in ji shi.
Wannan na nunar da gagarumar rashin jituwa tsakanin malaman jami'o'in Najeriya da gwamnatin tarayya da ta daɗe tana tufka da warwara.

Comments