Gwamnonin jam'iyar APC da masu takarar neman mukamin shugaban kasa sun ja daga akan wannan mataki na tsayar da Ahmad Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasa.
Sun nemi dole mulki ya koma kudu kuma a gudanar da zaben fidda gwani.
Labarin da ke shigowa yanzu haka ya nunar da cewa za a fafata a zaben fidda gwani tsakanin mataimakin shugaban kasa
Yemi Osinbajo da Asiwaju Bola Tinubu da Kayode Fayemi da David Umahi da sauran su a Dandalin Eagles da ke Abuja a gobe talata.
Za ku ji sauran bayani daga baya.
Comments