Skip to main content

"Ba Ni Goyon Bayan Kowane Dan Takara" - Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bauyana cewa bai zabo kowane dan takara ba, akan haka a bar daliget su zabi wanda 'yan jam'iyya ke so.

Bayan ganawa da shugaban kasan jim kadan bayan da shugaban jam'iyyar APC Sanata Abdullahi Adamu ya ayyana Sanata Ahmed Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasa na APC, karkashin jagorancin gwamnan jahar Kebbi Atiku Bagudo, sun ce sun tabbatar ma shugaba Buhari cewa har yanzu suna kan bakansu na mika mulki ga kudu.

Wannan dai ya nuna daga gobe takara jam'iyyar APC za ta gudanar da zaben fitar da gwani.

Comments