Tun bayan da wani matashi a birnin New York na Amurka, mai suna Hadi Matar ya sokawa marubucin wuƙa ya ke kwance a wani asibiti a birnin.
A jiya lahadi aka gurfanar da mista Mata a gaban wata kotu in da ya musanta laifukan yunƙurin kisan kai da ake zargin sa da yi. Alƙalin kotun Jason Schmidt ya bayar da umurnin ci gaba da tsare shi ba tare da bayar da beli ba har zuwa lokacin da za a sake gabatar da shi a gaban kotun.
Wani makusancin Salman Rushdie mai suna Andrew Wylie, ya sanar da cewa Mista Rushdie na cikin halin mutu-kwakwai-rai-kwakwai sakamakon munanan raunukan da ya samu bayan da aka daɓa ma sa wuƙa a fuska da wuya da kuma cikinsa, abinda ya kai ga taɓa hantarsa.
Kusan shekara 10 kenan Salman Rushdie na famar É“uya, tun daga lokacin da shugaban addinin Æ™asar Iran, Ayatullahi Ruhullah, ya bayar da umurnin a kashe shi tare da saka ladar dala miliyan 3 ga duk wanda ya kashe shi. Sannan a shekarar 2012 gwamnatin ta Farisa ta Æ™ara wasu dala 500,000 bisa ga na farko. Fitaccen marubucin dai ya wallafa wani littafi ne da yayi É“atanci ga Annabi (S.A.W.) da ya bayyana AlÆ™ur’ani mai girma da suna “Ayoyin ShaiÉ—an”. abinda kuma ya jawo hushin miliyoyin al'ummar musulmi a duniya.
Comments