Skip to main content

Shugaban Gwamnatin Jamus Frank-Walter Steinmeier Na Shan Suka

Jami'an Ukraine da na Poland sun soki shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier da cewa yana dasawa da  Rasha. Jakadan Ukraine a birnin Berlin ya kaurace wa wani bikin zaman lafiya da mawakan Rasha da Steinmeier ya shirya.
Gidan rediyon DW ya ruwaito cewa, Jakadan Ukraine a Jamus Andriy Melnyk da mataimakin firaministan Poland Jaroslaw Kaczynski  sun caccaki shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier sakamakon alakar da aka lura yana da ita da kasar Rasha.
Melnyk ya gaya wa jaridar Tagesspiegel cewa, "Steinmeier na da abin da ya ke boyewa dangane da wannan alaka tasa da Rasha".
Ya kara da cewa, "mutanen da ke da alaka da Steinmeier kamar Jens Plötner, mai ba wa Wazirin Jamus, Olaf Scholz shawara kan manufofin kasashen waje, da Sakatariyar Ma'aikatar Harkokin Wajen Jamus Andreas Michaelis hadi da karin wasu, na daga cikin wadanda ake zargin cewa ba za su rasa hannu ga wannan kusanci ba".
Kaczynski ya kuma bayyana cewa manufofin ketare na Jamus na da tasgaro in da bai gamsu da yadda ake tafiyar da su ba, a maimakon haka, ya yi kira da a kara yawan sojojin Amurka da ke nahiyar Turai da kashi 50 cikin 100 domin tunkarar matsalar tsaro da ke kunno kai a nahiyar.
Wannan furuci na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Jamus ke neman sauya salon siyasarta dangane da kasar Rasha, sakamakon mamayar da aka yi wa Ukraine.
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ƙara kashe kuɗin tsaron Jamus kimanin Euro biliyan 100 wanda wannan ya karya daɗaɗɗen abin da ya faru bayan yakin cacar baka don ba da agaji ga Ukraine.

Koda ya ke kasar Jamus din a hannu daya, ta yi abin a zo a gani in da ta yi maraba da kusan 'yan gudun hijirar Ukraine 300,000.

Melnyk ya ci gaba da cewa, "Wani abin takaici ma shi ne, Steinmeier ya taba samar da tashar yanar gizo ta musamman domin samar da ingantacciyar hanyar sadarwa tsakanin Jamus da Rasha shekaru da yawa", Ya kara da cewa, "a wurin Steinmeier, dangantakar kasarsa da Rasha ta kasance gagaruma mai mahimmanci - har ma da tsarki, duk kuwa da abinda ya faru, hatta mamayar da Rasha ta yi ma Ukraine babu wata alamar zai taka rawar a zo a gani ko ma ya yi tir da matakin."

Jakadan Ukraine a Berlin a baya ya fito fili ya soki Steinmeier ta hanyar kin gayyatar da aka yi masa zuwa wani bikin zaman lafiya da ya shirya tare da mawakan Rasha.

"A nawa ra'ayi, wasan kwaikwayon ya kasance wata alama ce mai yi wa Moscow dadi, watakila ma don tallata manufofin Putin," in ji Melnyk.

 Melnyk ya lura cewa gwamnatin Jamus ba ta fito ba game da raba shirye-shiryenta na isar da makamai.  Jakadan ya lura cewa ya karanta labarin cewa Jamus na shirin baiwa Ukraine makamai da kudinsu ya kai Euro miliyan 308, to sai dai babu wani abu zahiri da ya nuna hakan.

Shi kuma mataimakin firaministan kasar Poland Kaczynski ya ce, "Turai na bukatar karin sojojin Amurka saboda karuwar ta'addancin Rasha," ya kara da cewa Jamus na jan kafa ga Moscow."
newsweek.com
Sannan a cewar sa ya zama wajibi ga shugaba Olaf Scholz ya taka rawar a zo a gani domin samar da 'yanci ga kasashen turai".

Haka ma Kaczynski ya ce kasar Poland shirye ta ke ta tura makaman nukiliyar Amurka a yankinta, ko da yake ba a yi wata tattaunawa da Washington kan lamarin ba.

Comments

Wadanda aka fi karantawa

An Sako Ƙarin Fasinjojin Jirgin Ƙasa Bakwai Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Wasu fasinjoji bakwai da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa na ranar 28 ga Maris a jihar Kaduna sun samu 'yanci. An sako mutanen ne a safiyar Laraba bayan sun shafe kwanaki 135 a hannun ‘yan ta’addan. Sai dai ba a bayyana ko an biya kudin fansa ga 'yan ta'addar domin a sako su ba. Ɗaya daga waɗanda suka shiga sasantawar mai suna Tukur Mamu, ya fada  a wata sanarwa a ranar Laraba cewa shida daga cikin wadanda aka sako ‘yan gida daya ne, wadanda suka hada da ma’aurata da ‘ya’yansu hudu.  Sanarwar ta ce an sako yaran da iyayensu ne bayan da Sheik Ahmad Gumi ya shiga tsakani

Osinbajo Ya Fito Takarar Shugaban Kasa

A jiya ne mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana aniyarsa ta tsaya takarar shugaban kasar Najeriya a 2023. Ya fadi hakan ne a lokacin wani kwarya-kwaryar buda baki da ya halarta tare da wasu gwamnonin jam'iyyar APC da suka hada da na jahar Kebi Abubakar Atiku Bagudo da na Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i da sauran su. A yau litinin dai ne Osinbajo zai sanar da wannan kudiri nasa a dokance, ta wani jawabi da za a yada ta bidiyo. Idan ana iya tunawa dai watanni biyu da suka gabata mataimakin shugaban Najeriyar ya ce ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari wannan manufa tasa. Kafin bayyana wannan bukata, tuni dai wasu suka fito suka bayyana bukatar tsayawa takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC da suka hada da tsohon gwamnan jahar Legas, Bola Ahmed Tinubu da gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello da Rochas Okorocha da kuma kwanan nan ministan suhuri kuma tsohon gwamnan jahar Ribas, Rotimi Amechi da sauran su.