Ɗan jarida mutum ne kamar kowa, sai dai tunaninsa da manufofinsa kan tafi daidai ne kawai da ra'ayin MASU SAURARO ta fuskokin da suka shafi aikinsa. Ya zama mai wakiltar waɗanda ba su da baki ne ko kafafuwan zuwa, kuma idanuwan talakawa a kowane lokaci. Idan ka nuna ma sa launi shuɗi, ƙoƙarin ya ke ya tabbatar da launin nan shuɗi ne ziryan ko yana da garwaye? Idan ka ce ma sa labarin abu kaza ya faru, ba zai ce a'a ba kuma ba zai ce eh ba, aikinsa shi ne TABBATARWA . Idan mai sauraro namiji ne ko mace ko mai ra'ayin wani addini ko akida ko mai kuɗi ko talaka, ɗan jarida kan GIRMAMA kowa, kuma zai ɗauki kowa a matsayin DAIDAI ta fuskar ba su damar bayyana ra'ayoyinsu. Ɗan jarida kan tafi da zamani, ya kuma rungumi fasahar da ƘIRƘIRA ta kawo domin tafiya daidai lokaci. A kowace marra GASKIYA ita ce madogarar ɗan jarida, kuma wannan kan ƙara sa masu sauraro su amince da shi. Amma kuma, dole ne ɗan jarida ya zama MAI IKON KANSA , ba zai yi ma kowa alfarma b...
Comments