Skip to main content

INEC Ta Yi Watsi Da Lawan Ta Tabbatar Da Machina

Hukumar Zabe Mai Zaman Kan ta Najeriya (INEC) ta fitar da sabuwar sanarwa a jiya alhamis 23 ga watan Yuni, 2022 da ke tabbatar da Bashir Sheriff Machina a matsayin halastaccen dan takarar kujerar dan majalisar dattijai na kasa mai wakiltar kananan hukumomin Machina da Gashuwa da Nguru da Jakusko da Yusufari da Bade da kuma Karasuwa jahar Yobe, in da kuma ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa ba ta san da wani zaben fidda gwani da aka gudanar ba koma bayan wanda ya wakana a ranar 28 ga watam Mayu.
A cewar INEC babu wani dan takara da ta sani face Bashir Sheriff Machina.

Tun da farko dai Sanata Ahmad Lawan ne ke wakiltar wadannan kananan hukumomin, wanda hukumar ta bayyana da cewa ya nemi mukamin shugaban kasa a maimakon matsayin da ya ke akai yanzu haka na dan majalisar dattijai.
An dai jiyo shugaban jami'iyyar APC na kasa Abdullahi Adamu, a wata hira da sashen Hausa na BBC na bayyana cewa ba su san da wani ba sai sanata Ahmed Lawan, abinda ya jawo cece-ku-ce.
Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da 'yan takara da dama ke canza sheka tsakanin jam'iyu kuma ake samun irin wannan dambarwa kamar a jahr Kebbi in da sanata Adamu Aleiru ya canza sheka daga jam'iyar APC tare kuma da kwace takarar kujerar dan majalisar dattijai daga hannun Alhaji Haruna Sa'idu a lokaci guda kuma jam'iyyar ta kori Haruna Sa'idun tare da mika ma Sanata Adamu Aleiru tikintin takarar.

Comments

Wadanda aka fi karantawa

INEC Ta Nemi A Kama Kwamishinan Da Ya Sanar Da Sakamakon Zaɓen Adamawa

Bayan kammala wani zaman tattaunawa a jiya talata da Hukumar ta INEC ta yi a Abuja dangane da dambarwar da ta faru a jahar Adamawa.  Hukumar ta fitar da sanarwar matakin da ta ɗauka a shafinta na twitter, inda ta yi kira ga Sifetan 'yan sanda na ƙasa da ya gurfanar tare da tuhumar tsohon kwamishinan zaɓen jahar Barista Hudu Yunusa Ari. Ta kuma nemi Sakataren Gwamnatin Tarayya da ya ja hankakin hukumomin da ke da alhakin naɗa kwamishinonin zaɓe domin ɗaukar matakin da ya dace. Wannan dambarwar ta soma ne tun daga ranar Lahadi lokacin da kwamishinan zaɓen ya ayyana A'ishatu Ɗahiru Binani a matsayin wadda aka zaɓa gwamnar jahar Adamawa gabanin a kammala tattara sakamakon zabe.

Da Dumi Dumi An Ceto Yaran Da Aka Sace A Katsina

Sakataren gwamnatin jahar Katsina Alhaji Mustapha Inuwa ya fitar da sanarwar cewa an samu nasarar ceto daliban nan da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su daga makarantar kwanan ta Kimiyya da ke Kankara a jahar Katsina. Ya ce an ceto yaran su 340, kuma yanzu haka suna kan hanyarsu ta isowa jahar daga Tsafen jahar Zamfara. Ana sa ran gobe jumu'a za su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin daga bisani a sada su da iyayensu. Sauran bayani zai zo nan gaba.

Takalman Fir'auna

Takalman Zinariya na Fir'auna Tutankhamun, na daula ta 18 wadda ya yi mulki shekaru 1,300 kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Yanzu haka waɗannan takalman na nan a Gidan Adana kayan Tarihi na Masarautar Alƙahira da ke Misira 📷 Saliadeen Sicey