Skip to main content

Hukumar Lura Da Kafafe Watsa Labarai Ta Najeriya Ta Ƙwace Lasisin Gidajen Rediyo Da Talabijin 52

Shugaban hukumar ta NBC Malam Balarabe Shehu Illela ne ya sanar da hakan a yau jumu’a, in da ya bayyana cewa akwai ɗimbin bashin da ya kai naira biliya 2 da rara da ake biyar gidajen talabijin na African Independent Television (AIT) da Silver Bird Television da aka fi sani da (STV) tare da ƙarin wasu 52.
Shugaban hukumar ya ce dokar Najeriya mai Lamba CAP N11, Sashe na 10, ta shekarar 2004 ta ba hukumar NBC wannan dama, kuma tun a watan Mayun bana ne suka wallafa sunayen kafafe watsa labaran da suka kasa sabunta lasisinsu tare da umurtar su da yin haka a cikin mako biyu rak, ko su fuskanci wannan mataki na karɓe mu su lasisi.
Wannan matakin dai ana ganin shi ne irin sa na farko a tarihin Najeriya da ya shafi gidajen rediyo mallakar jahohi da masu zaman kansu.

Kazalika, masana na fassara shi da wani salon gwamnatin tarayya na yaƙar ‘yancin faɗar albarkacin baki.
Wasu daga gidajen rediyo da wannan dakatarwar ta shafa sun haɗa da Gidan Rediyon Rima na Sokoto da Rediyon Jahar Kebbi da na Zamfara da Rediyon Jahar Kaduna da Rediyon Jahar Jigawa da Rediyon Jahar Katsina da Na Legas da Imo da Ondo da na Kuros Riba da sauran su. 

Idan ana iya tunawa a kwanan baya Hukumar Lura da Kafafen Watsa Labarai ta Najeriya ta ci gidan rediyon Vision FM da gidan talabijin mallakar Media Trust tara, da kuma shan alwashin ladaftar da kafar watsa labarai ta BBC Hausa, a bisa abinda hukumar ta kira, wuce gona da iri wajen bayar da labaran da suka shafi tsaro.

Comments