Reuters
Rasha ta gargadi kasashen yammacin duniya da cewa za a dauki tsauraran matakin soji kan duk wani hari da za a kai a yankin na Rasha, tana mai zargin Amurka da manyan kawayenta da zagon kasa ga tsaron kasashen Turai ta hanyar tunzura Ukraine a fili ta kai wa Rasha hari.
Yunkurin mamayar da Rasha ta yi a Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, ya raba wasu miliyoyi da matsugunansu, ya kuma haifar da fargabar kazamin fada mafi muni tsakanin Rasha da Amurka, tun bayan rikicin makami mai linzami na Cuba a shekara 1962.
Watanni biyu tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine, a cikin 'yan kwanakin nan Rasha ta ba da rahoton wani jerin hare-haren da sojojin Ukraine suka kai a yankunan Rasha da ke makwabtaka da Ukraine, kuma ta yi gargadin cewa irin wadannan hare-haren na da hadari sosai.
Ukraine ba ta dauki alhakin kai tsaye ba, amma ta ce abubuwan da suka faru na mayar da martani ne, yayin da Rasha ta yi kakkausar suka ga kalaman da kungiyar tsaro ta NATO da Birtaniyya ta yi cewa ya dace Ukraine ta kai hari kan kayan aikin Rasha.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova ta shaidawa manema labarai a birnin Moscow cewa, "A kasashen yammacin duniya, suna kira a fili ga Kyiv da ya kai wa Rasha hari ciki har da amfani da makaman da aka samu daga kasashen NATO."
"Ban baki shawara ki kara gwada hakurin mu ba."
Fadar Kremlin ta ce kasashen Yamma - musamman ma Birtaniya, na yunkurin kai manyan makamai ga Ukraine wanda babbar barazana ce ga tsaron Turai.
Comments