Skip to main content

Barista Yunusa Ari Ya Yi Ɓatan Dabo

Dakataccen kwamishin hukumar zaɓe na jahar Adamawa, Barista Yunusa Hudu Ari, ya ranta cikin na kare jim kaɗan bayan da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya nemi a gudanar da cikakken bincike game da badaƙalar da ake zargin sa da ita.
Kakakin hukumar INEC Festus Okoye ne ya sanar da gidan talabijin na Channels haka.
Okoye ya ce su kansu ba za su iya cewa ina ya shiga ba saboda tun bayan faruwar lamarin ba ya ɗaukar kiran waya kuma sun ma daina jin ɗuriyarsa gaba ɗaya.

Da aka tambai shi ko akwai wani mataki da hukumar INEC za ta ɗauka kan wannan sabon lamari, sai ya ce, "ai wannan hakkin jami'an tsaron 'yan sanda ne na tabbatar da sun san inda yake. Idan har jami'an tsaro na buƙatar gurfanar da shi, su ne za su iya zaƙulo shi tare da gabatar da shi a gaban shari'a".

Hudu Ari dai ya sanar da sakamakon zaɓen gwamnan jahar Adamawa a ranar Lahadin makon jiya, inda ya ayyana A'ishatu Ɗahiru Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen tun gabanin a kammala tattara sakamakon ƙananan hukumomi 10 da suka rage.

Comments

Wadanda aka fi karantawa

Osinbajo Ya Fito Takarar Shugaban Kasa

A jiya ne mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana aniyarsa ta tsaya takarar shugaban kasar Najeriya a 2023. Ya fadi hakan ne a lokacin wani kwarya-kwaryar buda baki da ya halarta tare da wasu gwamnonin jam'iyyar APC da suka hada da na jahar Kebi Abubakar Atiku Bagudo da na Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i da sauran su. A yau litinin dai ne Osinbajo zai sanar da wannan kudiri nasa a dokance, ta wani jawabi da za a yada ta bidiyo. Idan ana iya tunawa dai watanni biyu da suka gabata mataimakin shugaban Najeriyar ya ce ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari wannan manufa tasa. Kafin bayyana wannan bukata, tuni dai wasu suka fito suka bayyana bukatar tsayawa takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC da suka hada da tsohon gwamnan jahar Legas, Bola Ahmed Tinubu da gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello da Rochas Okorocha da kuma kwanan nan ministan suhuri kuma tsohon gwamnan jahar Ribas, Rotimi Amechi da sauran su.