Ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin Kudu maso Gabas hatta a cikin makon da za a gudanar da babban zaɓen 2023.
Rahotanni daga yankin sun ce wasu da ba gano ba sun kashe Mista Oyibo Chukwu, ɗan takarar ɗan majalisar dattawa mazabar Enugu ta gabas a ranar Asabar, sa’o’i 48 kafin gudanar da zaɓen.
An kashe Chukwu ne tare da wasu magoya bayansa biyar a ƙaramar hukumar Awkunanaw ta Enugu a lokacin da yake dawowa daga wani gangamin yaƙin neman zaɓe.
Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar Labour, Chijioke Edeoga, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jam’iyyun siyasa na yi wa ‘ya’yan jam’iyyarsa kisan gilla, waɗanda ke ganin barazana ce ga bunƙasar jam’iyyar a jihar.
Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, ya fito ne daga yankin Kudu maso Gabas, wanda tashin hankali ya zama ruwan dare, tun kafin lokacin zaɓe.
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sha alwashin gurgunta zaɓen da ke tafe a yankin amma jami’an tsaro sun tabbatar wa mazauna yankin cewa za su yi duk mai yuwa domin shawo kan lamarin.
Har kawo yanzu dai rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ba ta mayar da martani kan lamarin ba, wanda Edeoga ya ce yana da alaƙa da siyasa.
Comments