Rahotanni sun ce an kashe mutane da dama tare da ƙona gidaje a rikicin da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a yankin Mai Tumbi da ke ƙaramar hukumar Mangu a jihar Filato.
Babban Daraktan Hukumar Tabbatar Da Wanzuwar Zaman Lafiya a Jihar Filato Joseph Lengmang, ya yi Allah wadai da lamarin, inda ya ce sun yi matuƙar baƙin ciki da yadda lamarin ya faru, inda rahotanni masu tayar da hankali suka nuna cewa matsalar tsaro ta tabarbare a yankin, lamarin da ya yi sanadin rasa rayuwa da dukiya mai ɗimbin yawa.
Comments