Gwamnan jahar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufai ya roƙi jama'a cewa kowa ya yi amfani da tsoffin kuɗi daga nan har shekara huɗu.
A cikin wani gajeren bidiyo mai tsawon minti huɗu da daƙiƙa talatin da bakwai, an ga gwamnan na bayyana cewa ya bayar da umurnin duk wani ɗan jahar da ke kasuwanci kada ya fasa amfani da tsoffin kuɗaɗe.
"Duk wani ɗan jahar Kaduna daga nan har shekara huɗu in dai an zaɓi APC, Uba zai mayar masa da kuɗinsa". In ji gwamna El-Rufai.
A cewarsa wannan saƙo ne daga ɗan takarar jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, wanda kuma in ji gwamnan da an zaɓi Tinubu zai sauya wannan tsarin canjin fasalin kuɗi nan take in da zai dawo da tsoffin da mutane ba su kai banki ba. Saboda haka ya umurci jama'a da kada kowa ya kai kuɗinsa banki.
Ya ƙara da cewa da zarar an zaɓe su, ya ɗauki alkawarin amsar kuɗin mutane ya tilasta Babban Bankin Najeriya CBN ya canza su musu da sababbi.
Ya ci gaba da cewa, "Ku gaya ma kowane ɗan kasuwa, ya karɓi tsohon kuɗi, Nasiru El-Rufai da Uba Sani da Bola Ahmed Tinubu, sun yi muku alkawari, in dai an zaɓe mu, wannan tsari za a canza shi a ba kowa iya lokacin da ya kamata ya canza kuɗinsa".
Wannan na zuwa kwana ɗaya da babbar kotun tarayya ta ba shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da Babban Bankin CBN umurnin kada su ƙara wa'adin amfani da tsoffin kuɗaɗe.
Sai dai kafin nan gwamna El-Rufai na cikin na gaba wajen ƙalubalanatar shugaban ƙasa da Babban Bankin CBN akan sauyin fasalin kuɗi da har ya jagoranci wata tawaga da ta haɗa gwamnonin jahohin Kogi da Zamfara in da suka gana da shugaban ƙasa kan wannan batu, kafin daga bisani su maka Bankin CBN da shugaban ƙasa kotu.
A na haka wasu gamayyar jam'iyyu 13 sun fito sun bayyana cewa za su janye daga shiga zaɓe mai zuwa muddin aka ɗaga wa'adin da Bankin CBN ya ƙayyade na amfani da tsoffin kuɗaɗe daga ranar 10 ga wannan wata na Fabrairu.
Ko a ranar jiya Talata ƙungiyar gwamnoni sun gana da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele da kuma shugaban Hukumar EFCC a fadar Villa akan batun da ya shafi ƙarancin kuɗi a hannun jama'a da kuma buƙatar a ƙara wa'adin amfani da tsoffin kuɗi, zaman da aka tashi baram-baram.
Comments