'Yan sa'o'i da fitar da Babban Bankin Najeriya CBN ya fitar da sanarwar cewa bankuna na iya amsar tsofaffin takardun kuɗin naira 500 da naira 1000 daga hannun jama'a, to sai dai Bankin na CBN ya yi amai ya lashe in da ya ce bai amince bankuna su amshi takardun kuɗin naira ga kowa ba sai dai mutum ya kai kuɗinsa da kansa kamar yadda aka tsara da farko.
Wasu fasinjoji bakwai da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa na ranar 28 ga Maris a jihar Kaduna sun samu 'yanci. An sako mutanen ne a safiyar Laraba bayan sun shafe kwanaki 135 a hannun ‘yan ta’addan. Sai dai ba a bayyana ko an biya kudin fansa ga 'yan ta'addar domin a sako su ba. Ɗaya daga waɗanda suka shiga sasantawar mai suna Tukur Mamu, ya fada a wata sanarwa a ranar Laraba cewa shida daga cikin wadanda aka sako ‘yan gida daya ne, wadanda suka hada da ma’aurata da ‘ya’yansu hudu. Sanarwar ta ce an sako yaran da iyayensu ne bayan da Sheik Ahmad Gumi ya shiga tsakani
Comments