Mage ta zauna ta yi jugum ta rasa abinda ke yi mata daɗi, ko ina sai karɓar saƙon zagi da suka take yi daga dabbobin dawa da suka kiwata ta da guminsu saboda yaƙi da ɓeraye.
An zargi Mage da ba wa ɓeraye damar sace daddawar jamhuriya ba tare da ɗaukar mataki ba. Ga shi kuma wa'adin mulkin Mage ya ƙare dole ta koma gefe ta zama ƴar kallo.
Shin ko me Mage zata yi don kawo ƙarshen ɓarnar ɓeraye da suka tara daddawar jamhuriya don gadar kujerar Mage?
Mage ta fesa fiya-fiya akan wannan daddawar miya, wanda yanzu haka ƙwari da ɓeraye suka gano Mage ta shirya ganin bayan su don haka suka haɗa kai domin yaƙar ta.
A baya kowane ɓera mai riƙe da ragamar mulki ya ci karensa ba babbaka. Ya yi mulkin mallaka da kama karya. Ya saci daddawar miya son ransa, ya yaƙi duk wanda ya ɗaga masa murya, ya halatta kansa rusa akurkin kaji ba bisa ƙa'ida ba, ya mallake shingayen ƙananan dabbobi ba bisa ƙa'ida ba.
Duk da babbar majalisar dokokin zartaswa ta hana su ba su yarda ba, amma a yanzu da mage ta sako su a gaba sai suka koma neman goyon bayan ƙananan dabbobin da a baya suka ce ko da tsiya ko da tsiya-tsiya sai sun mulke su.
Ko yaya za ta kaya tsakanin Mage da ɓeraye? Lokaci ne babban alƙali.
Comments