Skip to main content

Sheƙar Tsuntsu Da Ta fi Kowace Girma A Duniya

A kan samu irin wannan sheƙar tsuntsun a ƙasashe kudancin Afirka irin Botswana da Namibiya.
Abin mamaki shi ne wani ɗan ƙaramin tsuntsu ne mai suna Philetairus socius kan yi wannan sheƙa.
 Ta yi kama da saƙar zuma, kuma ya kan nemi bishiyoyi masu ƙarfi kamar gawo da bagaruwa da farar ƙaya sannan ya yi wannan sheƙa. Ta kan jure ruwan sama da zafin rana har ma da tsananin sanyin hunturu.
A cikin sheƙa ɗaya akan samu ɗakuna kamar ɗari, ƙofofin kusa da juna.
Masu nazarin rayuwar tsuntsaye na ganin wannan tsuntsu shi ne irin sa na farko a duniya ɗan ƙarami da kan gina sheƙa mai girma kamar wannan.
Faɗin sheƙar ya kan iya kai har ƙafa 20 tsawonta kuma ƙafa 10. 

Comments